An Nemi Mataimakin Gwamnan Kano da Ya Bi Kwankwaso Ya Yi Murabus

An Nemi Mataimakin Gwamnan Kano da Ya Bi Kwankwaso Ya Yi Murabus

  • Kwamishinan yada labaran Kano ya ce rashin goyon bayan mataimakin gwamna ga Abba Kabir Yusuf na iya jawo tangarda ga tafiyar gwamnati da hadin kai
  • Ya bayyana cewa ci gaba da zama a gwamnati tare da biyayya ga wata akida ta daban na iya haifar da shakku da rashin amana a matakin yanke shawara
  • Gwamnatin Kano ta jaddada cewa fifikonta shi ne ci gaban jihar, inda ta ce ba za a bar wani rikicin siyasa ya kawo cikas ga wannan manufa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Kwamishinan yada labaran Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bukaci mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya yi murabus daga mukaminsa matukar ba zai goyi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.

Kara karanta wannan

Bayan shiga APC, Abba zai kawo karshen rikicin Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Waiya ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi, inda ya yi tsokaci kan halin siyasar da ake ciki a jihar bayan sauya shekar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.

Ibrahim Abdullahi Waiya da Aminu Abdulsalam Gwarzo
Kwamishinan yada labarai a hagu, mataimakin gwamnan Kano a dama. Hoto: Ibrahim Abdullahi Waiya|Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai game da bayanin da kwamishinan ya yi ne a wani bidiyo da Muhasa TV and Radio ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kira ga matakaimakin gwamnan Kano

Ibrahim Waiya ya ce sabani a cikin gwamnati na iya rage tasirin shugabanci da haifar da rashin jituwa wajen tafiyar da al’amuran mulki.

A cewarsa, idan wani babban jami’i a gwamnati bai gamsu da alkiblar shugabanci ba, ya dace ya dauki matsaya karara domin kauce wa rudani

Ya ce abin da suke fata, kamar yadda suka ga wasu kwamishinoni da ba su gamsu ba suka yi murabus, shi ma mataimakin gwamna ya dauki irin mataki idan ba ya tare da gwamna.

Kara karanta wannan

Ana batun sauya shekar Abba, za a bayyana asalin wadanda suka ci amanar Kano

Waiya ya kara da cewa da shi ne ya ga ba zai iya zama da Abba Kabir Yusuf a APC da tuni ya tattara kayansa ya bar gwamnatin jihar.

Bukatar hadin kai a shugabanci

Rahotanni sun nuna cewa kwamishinan ya ce nasarar kowace gwamnati tana bukatar hadin kai, amana da manufa guda daga dukkan mambobinta.

Aminiya ta wallafa cewa ya bayyana cewa zama a majalisar zartarwa tare da shakku kan inda ake son kaiwa na iya janyo matsala mai girma a harkokin gwamnati.

Ya ce idan kana zaune a taron majalisar zartarwa ana tattauna yadda za a gina Kano, amma ana da shakku kan inda abubuwan da aka tattauna za su kai, to akwai matsala.

Duk da haka, ya ce idan mataimakin gwamnan ya ga zai iya ci gaba da aiki tare da gwamna a halin da ake ciki, hakan na nan a matsayin zabinsa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar da Kwankwaso ya yi fata Abba ya shiga maimakon hadewa da Ganduje a APC

Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso
Abba Kabir Yusuf tare da Rabiu Kwankwaso kafin gwamna ya sauya sheka. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Magana kan rikicin sarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta bayyana cewa tana daukar matakai domin ganin ta warware rikicin sarautar jihar.

Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana haka, inda ya ce za su bi hanyoyin da suka dace domin shawo kan lamarin.

Ya kara da yi wa mutanen Kano alkawarin samun cigaba sosai bayan sauya shekar Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng