Kwankwaso Ya Tuna Bibiyar Alkalan Kotun Koli da Ya Yi saboda Abba a Zaben 2019

Kwankwaso Ya Tuna Bibiyar Alkalan Kotun Koli da Ya Yi saboda Abba a Zaben 2019

  • Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya ce bai taba jin irin wannan cin amanar siyasa ba kamar yadda Abba Kabir ya yi masa
  • Kwankwaso ya bayyana haka ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP zuwa APC duk da kokarin da ya yi masa ya samu mulki
  • Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa ya tuna gwagwarmayar da ya yi ga Abba Yusuf domin ganin an samu nasara a zaben shekarar 2019

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa bai taba fuskantar cin amana irin na wannan karo ba.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne bayan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya kasance makusancinsa a siyasa, ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

'Tun farkon mulki ne': An fadi lokacin da Abba ya fara bijirewa Kwankwaso a Kano

Kwankwaso ya tuna wahalar da ya sha saboda Abba Kabir a 2019
Gwamna Abba Kabir da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Sai dai a wani faifan bidiyo da hadiminsa, Saifullahi Hassan, ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya ce da ya fi dacewa gwamnan ya koma jam’iyyar ADC maimakon APC.

Yadda zaben 2019 ya gudana a Kano

A zaben 2019, INEC ta bayyana zaben gwamnan Kano da aka gudanar ranar 9 ga Maris a matsayin wanda bai kammala ba, saboda tazarar kuri’u tsakanin manyan ‘yan takara biyu ta yi kasa da kuri’un da aka soke.

A wancan lokaci, Abba Kabir Yusuf, dan takarar jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u 1,014,353, yayin da Abdullahi Ganduje na APC ya samu kuri’u 953,522, inda tazara ta kai kuri’u 26,655.

Jimillar kuri’u 100,873 ne aka soke, lamarin da ya sa aka gudanar da zaben cike gibi a kananan hukumomi 28 na jihar Kano.

Bayan kammala zaben cike gibin, Ganduje ya samu nasara da kuri’u 45,876, yayin da Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’u 10,239.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi tone tone kan Abba, ya fadi alherin da Buhari ya masu

Sakamakon karshe ya nuna Ganduje ya tara kuri’u 1,033,695, yayin da Yusuf ya samu kuri’u 1,024,713.

A shekarar 2020, Kotun Koli ta yi watsi da karar da Abba Yusuf ya shigar, tare da tabbatar da nasarar Ganduje.

Kwankwaso ya sha damuwa kan cin amanar da Abba ya yi masa
Jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: @KwankwasoRM.
Source: Facebook

Yadda Kwankwaso ya sha wahala kan Abba

A shekarar 2023 kuma, Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar zama gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar NNPP, tare da gagarumin goyon bayan Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya.

Kwankwaso ya ce ya kai Abba Yusuf har gidajen alkalan Kotun Koli domin rokon adalci bayan rikicin zaben domin neman alfarma.

Ya kuma bayyana yadda tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim, ya kira shi cikin damuwa lokacin da rikicin zaben ya barke.

“Na tuna cewa a 2019, na kai shi gidajen dukkan alkalan Kotun Koli a Najeriya domin roko. Ni da shi mun je kauyuka da garuruwansu."
“A lokacin da labarin ya fara, Pius Anyim ya kira ni nan take. Na same shi a gida, bai ma kammala gaisuwa ba sai ya rike kansa saboda mamaki.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya magantu kan dalilan da Abba ya fada masa yayin shiga APC

- In ji Kwankwaso

Ganduje ya yi wa Kwankwaso tayin sulhu

An ji cewa tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirinsa na daidaitawa da Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje ya ce siyasa ta tanadi sassauci, kuma a matsayinsu na Musulmi, babu wanda bai dace a nemi sulhu da shi ba.

Ya yi magana game da batun shugabancin APC a Kano da makomar Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda Ganduje ya nuna akwai yiwuwar goyon bayan tazarce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.