Maganar boye ta fito fili: An gano dalilin da yasa Ganduje ya kada Abba a Kano

Maganar boye ta fito fili: An gano dalilin da yasa Ganduje ya kada Abba a Kano

Tun bayan da a hukumance aka bayyana Abdullahi Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a zaben 2019 da aka kammala, da yawa daga masu sa ido na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan sakamakon zaben. Sai dai duk da ba wai abun mamaki bane, inda wasu ke nuna amincewarsu da jin dadin sakamakon zaben, a hannu daya kuwa da yawa sun koka tare da nuna bakin cikinsu kan yadda sakamakon zaben ya kasance.

A bangaren wadanda lamarin bai yi masu dadi ba, da yawansu na son barar da gwamnatin Ganduje ne saboda gazawarta na ci gaba da bayar da ilimi kyauta ga dalibai kamar yadda gwamnatin Kwankwasiyya ta faro, da tura dalibai zuwa kasashen waje domin karin karatu; da ma dai yadda aka dauko batun cin hanci da rashawa; sai dai, maganar cin hanci za ta ci gaba da ruruwa a jihar ko ya aka so.

Sai dai kamar yadda Legit.ng Hausa ta tattara rahoto musamman daga jaridar Daily Trust, Kanawa sun zabi Ganduje akan Abba bayan sun yi kyakkyawan nazari kan wanda zai kula da arzikinsu da kuma harkokin addini da dai sauransu.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Buhari ya ki rattaba hannu kan wasu dokoki guda 5

Ganduje ya kada Abba a Kano
Ganduje ya kada Abba a Kano
Asali: Twitter

Zahirin gaskiya, da yawan jama'a ba wai suna kin Abba Gida Gida bane. Amma dai tarihin siyasar Kwankwaso da halayensa musamman kalamansa suka tilasta jama'a karkata ga bangaren siyasar Ganduje da har ta bashi nasara.

Amma dai ga wasu daga cikin dalilan da ya sa al'ummar Kano suka zabi Ganduje akan Abba.

1. Idan da ace Abba Gida Gida ne ya lashe zabe, jiha mai girma kamar Kano za ta iya shiga cikin rudani da rashin makoma a hannun shugaban da baida kwarewar shugabanci, wanda sai ya dauk dogon lokaci yana karantar lamuran jihar. A cikin hakane kuma Kwankwaso zai iya zama kafi-gwamna, lamarin da kowa ke nesantarsa. Kari kan hakan, da yawan Kanawa sun kalubalanci Kwankwaso na yi wa'adi ukku, kuma dai hakan ya dakile kakaba mulkin uban gida.

2. Sanin kowa ne, bibiyar wadanda suka yi mulki a baya da sauran tone-tone za su mamaye jihar idan har da PDP ce ta ci zabe. Kuma babu mai tabbacin ko za a kammaa ayyukan da gwamnatin Ganduje ta fara a jihar. Kuma da yawa na ganin Kwankwaso zai yi amfani da wannan damar ta kwasar kudin Kano domin daukar nauyin kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel