Yanzu-yanzu: INEC ta saki ranar da za'a kammala zaben jihar Kano, Sokoto, da sauran

Yanzu-yanzu: INEC ta saki ranar da za'a kammala zaben jihar Kano, Sokoto, da sauran

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta bayyana ranar da za'a gudanar da zaben zagaye na biyu a jihohin da ba'a ida kammala zaben gwamna ba.

Hukumar ta saki jawabin ne da yammacin Talata, 12 ga watan Maris, 2019 a birnin tarayya Abuja inda tace:

"Hukumar ta gana a yau, 12 ga watan Maris, 2019 kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni 29 da yan majalisun dokokin 991 a ranar 9 ga watan Maris. A duka, an sanar da zakaru a jihohi 22."

"Baturen zaben jihohin Adamawa, Bauchi, Benue, Kano, Plateau da Sokoto sun bayyana cewa zaben gwamnan bai kammalu ba. Saboda haka, za'a karasa zabukan ranar Asabar, 23 ga watan Maris, 2018."

KU KARANTA: Jerin sunayen sabbin gwamnoni da INEC ta sanar sun lashe zabe

A bangare guda, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa INEC ta sanar da sunayen 'yan takarar gwamna 22 a cikin jihohi 29 da aka gudanar da zabe a ranar 9 ga watan Maris.

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki tana da jihohi 13 yayin da babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) tana da jihohi tara.

Jihohin da ba a gudanar da zabukkan gwamnoni ba a wannan karon sune Edo, Kogi, Ondo, Ekiti, Anambra, Osun da Bayelsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel