Kwankwaso Ya Yi Magana kan Cewa Ya Hada Baki da Abba wajen Shiga APC
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf da muƙarrabansa za su yi nadamar barin jam’iyyar NNPP, yana mai cewa abin ya zo masa da mamaki
- Kwankwaso ya bayyana cewa sauya sheƙar da gwamnan Kano ya yi zuwa APC ba wani shiri ba ne tsakaninsu, yana mai cewa shi ma har yanzu yana jin abin kamar mafarki
- Jagoran NNPP ya kuma jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya tana nan daram a jihar Kano, tare da ƙoƙarin haɗa kai domin fuskantar halin da Najeriya ke ciki a nan gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa yana da tabbacin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da muƙarrabansa za su yi da na sanin ficewa daga jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso ya ce fitar gwamna Abba daga NNPP ta ba mutane da dama mamaki, har ma da shi kansa, inda ya ce yana jin abin kamar mafarki saboda irin yadda al’amura suka faru cikin gaggawa.

Source: Facebook
Sanata Kwankwaso ya fadi haka ne a hira da BBC Hausa bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC a hukumance.
Kwankwaso bai hada baki da Abba ba
Sanata Kwankwaso ya ce mutane da dama suna kallon ficewar gwamna Abba kamar wani tsari ne da aka shirya tun da dadewa, ko tsakaninsa da gwamnan, ko kuma tsakaninsa da wasu mutane a siyasa.
Ya ce shi kansa sau da dama ba ya iya yarda da abubuwan da ke faruwa, yana mai jaddada cewa babu wata yarjejeniya ko fahimta tsakaninsa da gwamna Abba dangane da sauya sheƙar.
A cewarsa, abubuwan da ke faruwa sun zo ne ba zato ba tsammani, kuma hakan ya sa jama’a ke ta yin hasashe iri-iri kan dalilan da suka sa gwamnan Kano ya bar NNPP.
A ranar Litinin, 26, Janairu, 2026, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma’a, 23, Janairu, 2023.
Maganar Kwankwaso a kan Ganduje
Kwankwaso ya ce ganin yadda tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC har ya ɗaga hannunsa, alama ce cewa gwamnan ya riga ya yi nisa.
Ya ce da Ganduje yana da “hannun ɗagawa” a siyasa, da ya ɗaga a zaɓen 2019 da na 2023, yana mai cewa hakan hujja ce da ke nuna cewa APC ba za ta kawo wa gwamna Abba kwanciyar hankali ba.

Source: Facebook
Kwankwaso ya ƙara da cewa yana da tabbacin cewa gwamna Abba da maƙarrabansa za su fuskanci zaman ƙunci a APC, kuma ko da bai dawo NNPP ba, nan gaba zai yi da na sanin matakin da ya ɗauka.
Makomar Kwankwasiyya da siyasar Kano
Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa tafiyar Kwankwasiyya tana nan daram, yana mai cewa har yanzu Kano tana hannun NNPP duk da sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya ce sun riga sun fara neman hanyoyin haɗa kai da sauran mutane domin ceto Najeriya daga halin da take ciki, yana mai jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya ba ta tsaya kan mutum ɗaya ba.

Kara karanta wannan
Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC
A cewarsa, duk ɗan Kwankwasiyya da ya koma Gandujiyya yana jin kansa kamar yana cikin kurkuku, amma da zarar ya dawo, zai samu kwanciyar hankali da nutsuwa a tafiyar siyasa.
Hidimar da Kwankwaso ya yi wa Abba
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana yadda ya zaga Najeriya yana nemawa Abba Kabir alfarma.
Kwankwaso ya ce ya dauki Abba Kabir zuwa wajen manyan mutane domin su yarda su mara masa baya tun a zaben shekarar 2019.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda gwamnan ya koma jam'iyyar APC ya hade da mutanen da ya kira makiya masu yi wa Kwankwasiyya hamayya.
Asali: Legit.ng

