Ministan Tinubu Ya Fadi Abin da Tarihi Zai Rika Tuna Abba da Shi kan Barin Kwankwaso

Ministan Tinubu Ya Fadi Abin da Tarihi Zai Rika Tuna Abba da Shi kan Barin Kwankwaso

  • Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi tsokaci kan matakin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na komawa jam'iyyar APC
  • Festus Keyamo ya yaba wa Gwamna Abba kan dawo wa APC, inda ya ce dawowarsa ta nuna kamar bai taba barin jam'iyyar ba
  • Ministan ya kuma bayyana yadda tarihi zai rika kallon Gwamna Abba kan rabuwa da NNPP wadda ubangidansa na siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi martani kan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano zuwa jam'iyyar APC.

Festus Keyamo wanda yake rike da kujerar minista tun bayan zaben 2019 yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa dawowarsa jam’iyyar APC mai mulki.

Festus Keyamo ya yabawa Gwamna Abba kan komawa APC
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo Hoto: Sanusi Bature D-Tofa, Festus Keyamo
Source: Facebook

Festus Keyamo ya bayyana hakan ne a wani rubutun da ya yi a shafinsa na X a ranar Talata, 27 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 a zauren Coronation Hall na fadar gwamnatin jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf, wanda a baya ya kasance mamba a APC kafin ya tsaya takara kuma ya lashe zaben gwamna na 2023 a karkashin jam’iyyar NNPP ya sauya sheƙar ne tare da wasu ’yan majalisar dokokin jihar Kano da kuma ’yan majalisar wakilai.

Gwamna ya fadi dalilin shiga jam'iyyar APC

Jaridar The Punch ta ce da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba ya ce dawowarsa APC ta ta’allaka ne kan buƙatar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bisa fahimtar juna da manyan masu ruwa da tsaki na siyasa a jihar.

Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa wannan mataki zai samar da yanayi na siyasa mai kwanciyar hankali a Kano, yana mai cewa hakan ba zai rage gudunmawar waɗanda suka taimaka wajen nasararsa a matsayin gwamna ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamna Abba na shiga APC, Ganduje ya fadi jagoran jam'iyyar a Kano

Gwamna Abba Kabir ya sauya sheka zuwa APC
Gwamna Abba Kabir na jawabi a wajen taron komawarsa jam'iyyar APC Hoto: Assadeeq Photography
Source: Facebook

Me Ministan ya ce kan komawar Abba APC?

Da yake mayar da martani kan sauya shekar, Festus Keyamo ya yi maraba da gwamnan zuwa jam’iyyar mai mulki.

Keyamo ya ce za a tuna da gwamnan ta hanya mai kyau saboda fifita jin daɗin al’ummarsa sama da biyayya ga kowa.

"Ɗan uwana, Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf, maraba da dawowa gida APC. Da irin manyan nasarorin da kake samu a Kano a matsayinka na gwamna mai ra’ayin ci gaba na gaske, kamar ba ka taɓa barin APC ba.”
“Tarihi zai rubuta cewa ka fifita jin daɗin al’ummarka sama da makauniyar biyayya ga kowa.”

- Festus Keyamo

Barau ya yi wa Gwamna Abba gata

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi murnar dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya sanar da sauya sunan ƙungiyoyin da ke tallata manufarsa a siyasa.

Barau Jibrin ya bayyana cewa sauyin sunan ya biyo bayan shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC, tare da nufin haɗa kai da juna domin ci gaban Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng