Abubuwan da Suka Faru yayin da Jita Jitar Sauya Shettima ke Neman Ɗaiɗaita APC
- Rikici na neman barkewa a APC yayin da ake ci gaba yada cewa Bola Tinubu zai sauya mataimakinsa, Kashim Shettima
- Shugabannin APC da matasan Arewa maso Gabas sun gargadi Bola Tinubu cewa cire Shettima daga tikitin 2027 matsala ne
- Rahoton ya nuna cewa rade-radin sauya Shettima sun hada da batun tikitin Musulmi-Musulmi, matsin lamba daga kasashen waje
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ana ci gaba da yada jitar-jitar cewa wai Bola Tinubu zai sauya mataimakinsa, Kashim Shettima kafin zaben 2027 da ake tunkara.
Wasu har sun fara jero sunayen Kiristoci daga Arewacin Najeriya cewa a cikinsu ne za a zabi daya domin maye gurbin Kashim Shettima.

Source: Twitter
APC ta yi magana kan jita-jitar sauya Shettima
Sai dai jam'iyyar APC a cikin wani sako da ta wallafa a X ta karyata rahoton da ake yadawa game da sauya Kashim Shettima.
Ganin lamarin ya fara wuce gona da iri, jam'iyyar ta yi magana kan rade-radin da ake yi na sauya Kashim Shettima a zaben 2027.
Jam'iyyar APC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ana shirin sauya Shettima daga matsayin mataimakin shugaban kasa a matsayin abokin takarar Bola Ahmed Tinubu kafin 2027.
1. Rikici ya barke yayin taron APC a Borno
Rigima ta barke a Maiduguri lokacin ake gudanar da taron sauraron jama'a na jam'iyyar APC a Arewa maso Gabas.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan ya fusata bayan ya shiga zauren taron ba tare da ganin hoton Shettima ba.
An rataye wani babban allo a bayan mimbari dauke da hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin yankin da manyan shugabannin jam’iyyar.
Sai dai abu guda ya fito fili, hoton Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, bai bayyana a ciki ba.
Lokacin da Lawan ya tashi magana, ba batun gyaran kundin tsarin mulki ya fi mayar da hankali ba, cike da takaici, ya tambaya:
“Me ya sa aka cire hoton Mataimakin Shugaban Kasa daga wannan allo?”

Source: Twitter
2. Rigimar da ta barke a Gombe kan Shettima
Ba wannan ne karon farko da hoton Shettima ya bace a taron APC a yankin ba, a bara ma, irin haka ta faru a Gombe, inda har ta rikide zuwa cacar baki da hargitsi.
Sai dai abin da ya faru a Maiduguri ya fi tasiri saboda gida ne ga Shettima, kuma ya zo ne a lokacin da ‘yan siyasa ke fara shirin tunkarar zaben 2027.
Yayin taron, Abdullahi Ganduje ya ki ambatar Shettima ba a jawabinsa, lamarin da ya haddasa rikici har aka rufe taron da wuri.
3. Kashim Shettima: Hatsarin da ke tunkaro jam'iyyar APC
Jigo a APC kuma masani kan harkokin tsaro, Abayomi Nurain Mumuni, ya gargadi cewa sauya Shettima bisa dalilin addini zai iya zama babban kuskure.
Mumuni, wanda ya taba zama cikin tawagar tsaro ta kamfen din Tinubu/Shettima a 2023, ya ce babu wani dan Arewa Kirista da ke da karfin siyasa, karbuwa da tasirin da zai maye gurbin Shettima.
Ya kara da cewa amana da jajircewa, siffofin da ya ce Shettima ya nuna, suna taimaka wa zaman lafiyar gwamnati.
A cewarsa, canza tikitin da ya yi nasara na iya karya hadin kai a APC da kuma rage karfin jam’iyyar a 2027.

Source: Twitter
4. Arewa maso Gabas ta yi martani
A Arewa maso Gabas, da dama na kallon batun cire Shettima a matsayin cin amana, wannan ra’ayi ya fito fili daga bakin kungiyar 'APC Youth Parliament'.
Shugabanta, Kabiru Garba Kobi, ya ce rade-radin sauya Shettima na iya janyo babbar asara ga Tinubu a yankin.
Kobi ya jaddada cewa Shettima shi ne ginshikin hadin kai a Arewa maso Gabas, kuma ya gargadi jam’iyya da kada ta saurari ‘yan siyasa masu yada rade-radin.
5. Arewa ta Tsakiya ta musanta rade-rade
Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta musanta jita-jitar cewa suna neman kujerar Mataimakin Shugaban Kasa, ta ce hankalinsu yana kan shugabancin kasa a 2031.
Kungiyar ta yi gargadi cewa cire Shettima zai rage kuri’un Tinubu kuma ya bai wa ‘yan adawa dama.
6. Minista ta yi gargadi kan 'sauya' Shettima
Ministar al’adu da tattalin arzikin kirkire-kirkire, Hannatu Musawa ta gargadi APC kan sauya tikitin Tinubu–Shettima kafin 2027.
Hannatu Musawa ta ce sauyin zai iya jawo asarar kuri’u a Arewacin Najeriya kuma akwai barazanar cewa ba za a kai labari ba.
Ta bayyana cewa siyasar Arewa tana da tsari na musamman, kuma dole a nazarce shi da kyau kafin yanke hukunci.

Source: Twitter
7. Shiru daga bangaren Kashim Shettima
Har yanzu Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, bai ce uffan ba kan bacewar hotonsa ko rade-radin siyasa da ake yadawa.
Sai dai a siyasar Najeriya, shiru wani lokaci dabara ce, wani lokaci kuma alamar abin da ke tafe zai iya zama gaskiya, cewar Vanguard.
Abin da ya fara daga bacewar hoto a Maiduguri, yanzu ya zama kokwanto game da biyayya, iko da makomar APC gabanin 2027.
8. Matsin lamba daga kasashen waje
Wasu majiyoyi daga fadar Aso Rock sun ce ana fuskantar matsin lamba daga kasashen waje, musamman Amurka, kan batun daidaiton addini a Najeriya.
Kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, kan tsangwamar Kiristoci a Najeriya sun kara rura wutar muhawara, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.
Wasu ‘yan APC sun ce tsarin tsaro na kasar nan ya riga ya nuna daidaito, yayin da wasu ke kin amincewa da tsoma bakin kasashen waje a harkokin zaben Najeriya.
Fasto ya yi hasashen sauya Shettima da gwamna
A baya, kun ji cewa limamin addinin Kirista, Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin sauya Kashim Shettima kafin zaben 2027.
Malamin ya yi gargadin barazanar rikici a APC idan har shugaban ya yi yunkurin sauya Shettima daga mukaminsa.
Ayodele ya ce cire Shettima cikin rikici zai iya janyo masa aiki da muradun APC, yana mai cewa gwamna ne ake shirin dauka a madadinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




