An Fara Siyasa: Barau Ya Sauya Sunan Kungiyarsa bayan Abba Kabir Ya Koma APC
- An karɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC a gidan gwamnatin Kano, inda aka yi kira ga goyon bayan sa domin ci gaban jihar
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya sanar da sauya sunan ƙungiyoyin da ke tallata manufarsa zuwa 'Tinubu, Abba, Barau'
- Tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya bayyana shigowar Abba Kabir Yusuf a matsayin sauyi mai muhimmanci a siyasar Kano
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Jam’iyyar APC ta karɓi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, cikin jam’iyyar a wani taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.
A yayin taron, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya yi jawabi inda ya nuna farin ciki da shigowar gwamnan jam’iyyar, tare da yin kira ga magoya bayansa da masu tallata shi su mara wa gwamnan baya.

Source: Facebook
Bayan taron, Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya sauya sunan kungiyarsa da ke tallata shi da Bola Tinubu.
Sabon sunan kungiyar Barau Jibrin
Bayan taron karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya sanar da sauya sunan ƙungiyoyin da ke tallata manufarsa a siyasa.
A cewarsa, ƙungiyoyin da a baya ake kira Tinubu/Barau Organisation yanzu za su riƙa amfani da suna Tinubu, Abba, Barau Organisation.
Barau Jibrin ya bayyana cewa sauyin sunan ya biyo bayan shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC, tare da nufin haɗa kai da juna domin ci gaban Kano.
Ya ce a yayin da yake maraba da gwamnan cikin jam’iyyar, ya buƙaci dukkan magoya bayansa da masu tallata shi su tsaya a layi guda tare da gwamnan domin ganin an cimma muradin ci gaban jihar.

Kara karanta wannan
Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC
Barau ya ce Kano sai Abba a 2027
A cewar Barau Jibrin, lokacin da ya ambanci 'Najeriya' a wurin taron, jama’a suka amsa da “Sai Tinubu”, yayin da ya ambaci 'Kano' aka biyo da amsa “Sai Abba Gida-Gida”.
Ya bayyana hakan a matsayin alamar goyon bayan jama’a ga shugabancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa shigarsa siyasa sama da shekaru 30 da suka gabata ta samo asali ne daga ƙudirin yi wa al’ummar Kano da ƙasar nan hidima.

Source: Facebook
Tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya wallafa a X cewa ranar ta zama wata muhimmiyar alama a siyasar Kano, ganin yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yanke shawarar shiga jam’iyyar APC.
Abba ya saka hotunan Ganduje a Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa a jiya Litinin, 26 ga Janairun 2026 aka sanya hoton jagororin APC a gidan gwamnatin jihar Kano.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Gwamna Abba na shiga APC, Ganduje ya fadi jagoran jam'iyyar a Kano
Hadiman Abba Kabir Yusuf da sauran 'yan siyasa sun saka hotunan shugaba Bola Ahmed Tinubu, Abdullahi Umar Ganduje da sauransu.
Rahotanni sun nuna cewa an yi hakan ne a shirin karbar Abba Kabir Yusuf da ya fita daga jam'iyyar NNPP zuwa APC ma mulki a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
