Ministan Tinubu Ya Fadi Mafitar da Kwankwaso ke da Ita bayan Tafiyar Abba

Ministan Tinubu Ya Fadi Mafitar da Kwankwaso ke da Ita bayan Tafiyar Abba

  • Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce Rabiu Musa Kwankwaso ya takaita wa kansa hanyoyin siyasa bayan kin amincewa da shiga APC a baya
  • Keyamo ya bayyana cewa burin Kwankwaso na zama shugaban kasa ne ke rikitar da shi, musamman ganin manyan jam’iyyu na da nasu tsare-tsare gabanin 2027
  • A cewarsa, zabin da Kwankwaso zai yi a 2027 zai iya zama wanda zai raya akidar Kwankwasiyya ko kuma ya kawo karshen burinsa na siyasa a kasa baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya tsinci kansa cikin daya daga cikin mafi tsananin mawuyacin hali a rayuwarsa ta siyasa.

A cewarsa, babban abin da ke kawo rudani shi ne burin Rabiu Kwankwaso na tsayawa takarar shugaban kasa, wanda ke fuskantar manyan kalubale daga jam’iyyun siyasa masu karfi a kasar.

Kara karanta wannan

Abba: Gwamnatin Kano ta yi wa Kwankwaso guzar zana kan tasiri a siyasa

Rabiu Kwakwaso tare da Festus Keyamo
Rabiu Kwankwaso da Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo. Hoto: Saifullahi Hassan|Festus Keyamo
Source: Facebook

Keyamo ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a X, inda ya ce duk da cewa ya dade yana girmama Kwankwaso, sababbin sauye-sauyen siyasa sun rage masa tasirin da zai iya yi gabanin zaben 2027.

Matsalar Kwankwaso a 2027 inji Keyamo

Minista Festus Keyamo ya ce Kwankwaso na son zama shugaban kasa, amma babu wata babbar jam’iyya da za ta ba shi tikiti a 2027.

Keyamo ya bayyana cewa APC da PDP sun karkata tikitinsu zuwa Kudanci, yayin da jam’iyyar ADC kuma ke karkashin tasirin Atiku Abubakar.

Ya kara da cewa jam’iyyar NNPP, wadda Kwankwaso ke jagoranta, har yanzu jam’iyya ce ta jiha daya, kuma da yawan ficewar manyan jiga-jiganta, ciki har da gwamna, akwai shakku kan ikon jam’iyyar na rike Kano a 2027.

Alakar siyasar Arewa da Kwankwaso

Ministan ya ce Kwankwaso ba zai goyi bayan dan Arewa a zaben 2027 ba, domin hakan zai rufe masa kofar burinsa na shugaban kasa na tsawon shekaru masu yawa.

Kara karanta wannan

Lamura na ƙara dagulewa Abba Kabir, kwamishina a gwamnatinsa ya yi murabus

Ya bayyana cewa idan dan Arewa ya yi mulki, Kwankwaso zai jira akalla shekaru 16 kafin sake samun damar tsayawa takara a Najeriya.

Keyamo ya ce wannan kasada ce Kwankwaso ba zai dauka ba, ganin cewa zai kai kimanin shekaru 86 a wancan lokaci. Saboda haka, a cewarsa, wannan dalili ne ya kawar da yiwuwar hadin gwiwar Atiku da Kwankwaso a 2027.

Mafitar da Kwankwaso ke da ita

Punch ta rahoto cewa Keyamo ya ce zabin Kwankwaso na hadin kai yanzu ya takaita zuwa jam’iyyun PDP, APC ko LP, amma kowanne na dauke da kalubale.

A kan PDP, ya ce Kwankwaso na iya dawowa da sharuda, kamar karbe tsarin jam’iyyar a Kano, amma hakan zai janyo rugujewar NNPP tare da dakatar da burinsa na 2027 zuwa 2031.

Game da APC, Keyamo ya ce Kwankwaso ba shi da damar shimfida sharuda masu yawa, ganin yadda APC ke kara karfi a Kano. Duk da haka, APC na da tsarin kasa baki daya wanda zai iya taimaka masa a 2031.

A bangaren LP, Keyamo ya ce Kwankwaso ba zai amince ya zama mataimaki ga Peter Obi ba, kuma mabiyansa ba za su goyi bayan tsawaita mulkin Kudanci ba.

Kara karanta wannan

Badaru ya gana da Kwankwaso bayan ficewar Abba daga NNPP? An gano gaskiya

Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso
Wani lokaci da Abba Kabir ya karrama Rabiu Kwankwaso a baya. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Mawakin Kwankwasiyya ya yi sabuwar waka

A wani labarin, kun ji cewa ana cigaba da tattauna batun siyasar Kano bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba hanya da Rabiu Kwankwaso.

Shugaban mawakan Kwankwasiyya, Tijjani Husaini da aka fi sani da Tijjani Gandu ya saki sabuwar wakar nuna goyon bayan Kwankwaso.

A wakar da ya yi, Tijjani Gandu ya nuna cewa duk wani abu da za a yi na bijirewa Kwankwaso ba zai shiga ciki ba tare da mutanensa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng