Kano Ta Dauki Zafi, Gwamna Abba Ya Kori Hadiminsa bayan Ya Koma Tsagin Kwankwaso
- Siyasar jihar Kano na ci gaba da daukar zafi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP a jiya Juma'a
- Gwamna Abba ya sallami mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Sanusi Surajo Kwankwaso daga mukaminsa, kuma ya maye gurbinsa nan take
- Wannan mataki na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Sanusi ya saki wani faifan bidiyo da ke nuna cewa ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin jihar Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kori mai ba shi shawara kan harkokin siyasa Sunusi Surajo Kwankwaso, daga kan mukaminsa nan take.
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da haka yau Asabar, 24 ga watan Janairu, 2025.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya kori hadiminsa nan take
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kakakin gwamnan Kano ya ce Abba ya kori Sanusi Kwankwaso daga mukaminsa, sannan ya maye gurbinsa da Mustapha Bakwana.
Sanusi Bature ya ce:
"Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kori mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, ya maye gurbinsa da Mustapha Bakwana."
Hadimin gwamnan ya ajiye aiki tun farko
Wannan na zuwa ne bayan Sanusi Surajo Kwankwaso ya sanar da cewa ya ajiye mukaminsa a gwamnarin jihar Kano, tare da tabbatar da cewa yana tare da jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.
Tsohon hadimin gwamnan ya fadi haka ne a wani faifan bidiyo da aka saki ranar Juma’a 23 ga watan Janairu, 2026, wanda Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cikin bidiyon, Sunusi Surajo ya bayyana cewa ya yanke shawarar ajiye aiki ne bayan samun rahotanni masu karfi da ke nuna cewa Gwamna Abba ya fita daga jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan
Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso
Ya ce tun da farko ya rubuta takardar murabus ya mika, amma ba a karba ta a hukumance ba, lamarin da ya sa ya yanke shawarar fito ya sanar da murbaus dinsa ta bidiyon.

Source: Facebook
Gwamna Abba Kabir ya maye gurbinsa
Sai dai kasa da sa'o'i 24 bayan fitar wannan bidiyo, aka samu labarin Gwamna Abba ya kori Sansui daga matsayinsa na mai ba shi shawara kan harkokin siyasa.
Duk da babu wani cikakken bayani kawo yanzu, Sanusi Bature ya tabbatar da cewa an maye gurbinsa da Mustapha Bakwana, kuma matakin zai fara aiki nan take.
'Yan Kwankwasiyya sun gindaya sharudda
A wani rahoton, kun ji cewa wasu kungiyoyin matasan Kwankwasiyya a Jihar Kano sun bayyana aniyarsu ta bin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya fice daga jam'iyyar NNPP.
Sai dai kungiyoyin sun ce ba za su bi wannan tafi iso rufe ba, su na da sharuddan da za a cika masu kafin su amince su bar jam'iyyar NNPP gaba daya.
Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da matasa a Kano, wakilan kungiyoyin Kwankwasiyya sun ce ba su da matsala da Gwamna Abba a matsayin mutum.
Asali: Legit.ng
