‘Abin da Na Fada wa Gwamna Abba game da Butulce wa Kwankwaso' Inji Sanatan NNPP

‘Abin da Na Fada wa Gwamna Abba game da Butulce wa Kwankwaso' Inji Sanatan NNPP

  • Sanata Rufai Sani Hanga ya yi magana kan zargin cewa yana daga cikin masu tayar da rigimar da ta janyo ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Dattijon 'dan siyasar ya ce ya sha kokarin sasanta Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso, har ya ba gwamnan shawara domin a koyaye
  • 'Dan majalisar ya bayyana cewa Kwankwaso ya nuna damuwa kan halin da Abba ya shiga, yana mai cewa ba wannan Abban da ya sani ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ana ci gaba da kama layi bayan ficewar Abba Kabir daga jam'iyyar NNPP wanda ya rikita siyasar Kano.

Sanata Rufai Sani Hanga na daga cikin jiga-jigan NNPP da ya bayyana matsayarsa game da rigima da ta barke bayan murabus din gwamnan daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni 2 sun yanke shawara, sun zabi wanda za su bi tsakanin Abba da Kwankwaso

Sanata ya magantu kan rigimar Kwankwaso da Abba tun farko
Sanata Rufai Hanga yayin ganawa da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Sanata Hanga ya tona rigimar Abba da Kwankwaso

Wakilin Legit Hausa ya samu wannan matsaya ta Rufai Hanga ne yayin hira a wani faifan bidiyo da Express Radio ta wallafa a Facebook.

Ana zargin Sanata Hanga na daga cikin wadanda ke kitsa rigimar wanda ake ganin ita ce dalilin matsayar da gwamnan ya dauka.

Sai dai Sanata Hanga ya karyata hakan da cewa:

"To gaskiya ba haka ba ne, idan muka yi kokari muka hada shi fada da Kwankwaso meye ribarmu, meye za mu samu.
"Mu gyara muke yi tsakanin Kwankwaso da Abba, ni na ba Abba shawara tun a baya lokacin Abba tsaya da kafarka, na ce masa masu wannan abin ba masoyanka ba ne.
"Shi a lokacin ya yi fushi ya yi ta maganganu da yawa, daga karshe na ja kunnensa cewa Abba ka tuna kai ba yaro ba ne ka da a yaudare ka da Abba gida gida ka ce ko ka kawo karfi, Kano ba haka take ba."

Kara karanta wannan

2027: Ana so Kwankwaso ya hada kai da Barau su kifar da Abba a Kano

Yadda ya yi kokarin sasanta Abba da Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Hanga ya fadi kokarinsa a sasanta Abba, Kwankwaso

Sanata Hanga ya bayyana yadda ganawarsu ta kaya da Abba da kuma kokarin ganin an sasanta shi ga Rabiu Kwankwaso.

A cewar 'dan majalisar, Kwankwaso ya koka game da yadda gwamna ya daina daukar wayar shi kuma ya guje wa haduwa da shi.

Ya ce:

"Na ce wa jagora na samu Abba da cewa akwai rashin fahimta amma ya gane, shi kuma ya tambayen mai jagora ya ce, na ce jagora ya ce bai san matsalar ba, ba ka zuwa wurinsa ba ka daga wayarsa.
"Jagora ya ce sanata kusa a yi wa Abba addu'a, yadda nake ganin 'da na Mustapha haka na ke kallonsa, watakila ko an yi masa wani abu ne, ka da a cuce shi.
"Jagora ya ce wannan ba Abban da na sani ba ne, babu yadda za a yi ina son na gan shi amma bai yadda mun hadu ba kuma bai zo ba, idan zan je sai ya gudu."

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fallasa yadda aka zuga Abba kan rabuwa da Kwankwaso

Hadimin Abba Kabir ya yi murabus

An ji cewa Sunusi Surajo Kwankwaso ya yi murabus daga mukaminsa na mai ba Gwamnan Kano shawara ta musamman a kan siyasa.

Murabus din ya biyo bayan rahoton ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP, inda ake sa ran zai koma APC.

Alhaji Sunusi Kwankwaso ya jaddada biyayyarsa ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya domin ci gaba da inganta siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.