Sanata Rufai Hanga yace an tafka magudi a zaben Jihar Kano

Sanata Rufai Hanga yace an tafka magudi a zaben Jihar Kano

Rufai Sani Hanga wanda ya taba zama ‘Dan majalisar dattawa na yankin Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar ANPP da ta shude ya bayyana irin abin da ya auku a zaben jihar Kano da aka yi.

Sanata Rufai Hanga wanda yayi wa jam’iyyar PDP mai adawa aikin Wakilin zabe a cikin karamar hukumar Madobi, ya bayyana an yi amfani da jami’an tsaro wajen tarwatsa wadanda su ka fito yin zabe a rumfunan akwatin gari.

Rufai Hanga yake cewa wani babban Kwamishina a gwamnatin Abdullahi Ganduje ya zo da wasu ‘yan sanda inda aka rika fatattakar Bayin Allah masu shirin kada kuri’a sannan kuma aka yi gaba da kayan zaben da aka kawo.

KU KARANTA: Zaben cike-gurbi: APC ta rufe ratar da Tambuwal ya bada a Sokoto

‘Dan majalisar yace an kuma kori Turawan zaben da su ka zo sa-ido a cikin Unguwar Mazabar kafin-agoro da ke cikin Garin na Madobi. Karamar hukumar Madobi dai nan ce Mahaifar tsohon gwamna Injiniya Rabiu Kwankwaso.

A jawabin da ‘dan majalisar yayi a fillin zaben, ya bayyanawa Duniya cewa wasu ‘yan iskan gari sun rika dangwale takardun kada kuri’ar a madadin jama’a. Sanatan yace an kuma harbe wasu motocin ‘yan jam’iyyar adawa a Yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel