'Ka Yi Hattara,' An Fadawa Tinubu abin da Zai Faru idan Ya Sauya Shettima a 2027

'Ka Yi Hattara,' An Fadawa Tinubu abin da Zai Faru idan Ya Sauya Shettima a 2027

  • Wata kungiyar APC ta gargadi Shugaba Bola Tinubu kan shirin maye gurbin Kashim Shettima da wani Kirista daga Arewa a zaben 2027
  • Shugaban kungiyar, Kabiru Kobi ya ce sauya mataimakin shugaban kasar zai iya janyo rugujewar APC da rashin nasarar Tinubu a zaben mai zuwa
  • Wannan na zuwa ne bayan fitar rahotanni kan cewa Tinubu na nazarin wasu Kiristoci 4 daga Arewa don zabar abokin takara daga cikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Wata kungiyar matasan APC ta shiyyar Arewa maso Gabas ta gargadi Shugaba Bola Tinubu kan rade-raden maye gurbin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Shugaban kungiyar, Kabiru Kobi, a hira da Legit Hausa ya bayyana cewa kokarin sauya Shettima zai iya kawo cikas ga nasarar Tinubu a yayin da zai nemi tazarce a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Dogara da Kiristoci 3 da ake sa ran Tinubu zai maye gurbin Shettima da su a 2027

An gargadi Tinubu kan sauya Kashim Shettima a zaben 2027
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (hagu), Kabiru Kobi, shugaban kungiyar matasan APC (tsakiya), da Kashim Shettima (dama). Hoto: @officialABAT, @KashimSM
Source: Twitter

Batun zaben sabon abokin takarar Tinubu

Wannan gargadin ya biyo bayan rahoton jaridar The Guardian da ya nuna cewa ana nazarin wasu jiga jigan Kiristoci hudu a Arewa don zabar abokin takarar Tinubu daga cikinsu.

Sunayen da ake ambata sun hada da Yakubu Dogara, Christopher Musa, Caleb Mutfwang, da Bishop Matthew Kukah a matsayin wadanda za su iya maye gurbin Shettima.

Rahotanni sun nuna cewa na kusa da shugaban kasar suna bincike kan wadannan mutanen ne domin samar da daidaito tsakanin addini da kuma yanki a kasar gabanin 2027.

Martanin matasan Arewa kan sauya Shettima

Kabiru Kobi ya bayyana cewa wadannan rade-raden suna janyo rashin natsuwa a cikin jam'iyyar APC, wanda hakan zai iya janyo rabuwar kai gabanin zabukan masu zuwa.

Kobi ya gargadi masu ruwa da tsaki da su koyi darasi daga kurakuran baya, inda ya buga misali da yadda jam'iyyar PDP ta sha kasa a 2023, duk don saboda rikici kan takara.

Kara karanta wannan

Barazanar Bello Turji ta sa 'yan Najeriya gudun hijira Nijar, suna mawuyacin hali

Shugaban matasan ya ce:

"Muna so mu bayyana karara cewa duk wani yunkuri na sauya tikitin Tinubu da Shettima a 2027 zai janyo bacin rai daga magoya baya da masu kishin Arewa.
"Ko a 2023, mun zabi jam'iyyar APC ne saboda hadin da suka yi na Tinubu da Shettima, mun dora kyakkyawan yakini kan mutanen biyu, kuma ba su bamu mamaki a mulkinsu ba.
"Yanzu da ake cewa za a sauya Shettima da wani Kirista daga Arewa, za mu iya cewa wani shiri ne kawai na marasa kishin Arewa, domin idan da da gaske Arewa suke so, to babu dalilin sauya Shettima.
"Daga cikin dukkan wadanda ake cewa za a iya zaba madadin Shettima, fada mun, waye 'yan Arewa suka gamsu da nagartarsa, waye a cikinsu ya yi wani abun a zo a gani da zai jawo APC ta samu kuri'un Arewa? Babu! Don haka Shettima din dai shi ne zabinmu, shi ne zabin yawancin 'yan Arewa, don shi ne suka san amfaninsa."

Kara karanta wannan

Kano da wasu jihohin Najeriya 4 da siyasarsu ke ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027

Makarkashiyar siyasa da hadarin da ke ciki

Alhaji Kabiru Garba Kobi ya yi tambayar ko jam'iyyar APC za ta iya tsira daga makarkashiyar wasu mutane daga ciki wadanda ke son ruguza nasarorin da aka riga aka samu.

Ya ce:

"Shin ya kamata mu bari wasu tsiraru su rika yanke mana hukunci ba tare da an yi shawara da kowa ba? Mun yarda shugaban kasa na da 'yancin zabar abokin takararsa, amma kin tafiya da wanda al'umma ke so na iya jawo rashin nasararsa a 2027.
"Kuma ya kamata shugaban kasarmu, Baba Tinubu ya fahimci cewa, masu sukar kujerar Shettima tamkar shi suke suka. Abin da 'yan adawar nan suke so shi ne su sanya shi ya sauya Shettima da wani rubabben dan siyasa da zai iya jawo nakasu ga jam'iyyyar APC."
Kungiya matasan APC ta ce tana goyon bayan Tinubu da Shettima a 2027
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da Kabiru Kobi, shugaban kungiyar matasan APC, Arewa maso Gabas. Hoto: @officialSKSM/X, UGC
Source: UGC

Goyon baya ga takarar Tinubu da Shettima

Kungiyar matasan ta lashi takobin ci gaba da hada kan al'umma don ba da goyon baya ga Tinubu da Shettima, inda ta bayyana su a matsayin wadanda aka gwada kuma aka gamsu da ingancinsu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu bai dawo ba, jirgin Shettima ya shilla zuwa kasashe 2

"Mun gamsu da Tinubu da Shettima, kuma za mu zagaya lungu da sako na Arewa maso Gabas don ganin mun nema masu kuri'u a 2027, saboda mun gamsu da shugabancinsu.
"A tarihi ma, ba a taba samun shugaban kasa da mataimakinsa da suke aiki kafada-da-kafada ba irin Tinubu da Shettima, har yau ba ka taba jin an ce wai ga su suna sa'in'sa ba.
"Sauya Shettima a 2027 zai zama babbar barazana ga APC, gwanda mu sake nanata masu don su san irin abin da suke shirin aikatawa da ka iya ruguza batun tazarcen shugaban kasa."

- Alhaji Kabiru Kobi.

Kungiya ta soki Babachir kan taba Shettima

A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar matasan APC, reshen Arewa maso Gabas (APC-YPNE) ta caccaki Babachir Lawal saboda kalamansa kan Kashim Shettima.

Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi ya zargi Babachir da raina Shettima tare da nuna kiyayyarsa a fili kan tikitin Muslima Muslmi na 2023.

A zantawarsa da Legit Hausa, Kobi ya ce hassada ce kawai ke cin Babachir, kuma yana ji yana gani Shettima zai kara daukaka a gwamnatin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com