Kano da Wasu Jihohin Najeriya 4 da Siyasarsu Ke Ɗaukar Zafi gabanin Zaɓen 2027
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano na shirin sauya sheka zuwa APC, duk da rashin amincewar uban gidansa, Sanata Rabiu Kwankwaso
- Rikicin Nyesom Wike da Siminalayi Fubara ya jefa Rivers cikin rudani inda a yanzu haka 'yan majalisar dokoki ke kokarin tsige gwamna
- A wannan rahoto, mun yi bayani dalla dalla game da wasu jihohin Najeriya biyar da siyasarsu ta riga ta dauki zafi tun gabanin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Duk da cewa har yanzu hukumar INEC ba ta fitar da jadawalin zaɓen 2027 ba, amma a fili yake cewa harkar siyasa a Najeriya ta riga ta kankama.
A Kano da Rivers da wasu jihohi uku, kawance tsakanin tsofaffin gwamnoninsu da na yanzu ya riga ya rushe, yayin da aka kafa sabon lissafi.

Source: Twitter
2027: Jihohin da siyasarsu ta dauki zafi
Wannan rahoto, zai mayar da hankali ne kan jihohi Najeriya biyar, da siyasarsu ke ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027, kamar yadda BBC Hausa ta rahoto.
1. Jihar Kano

Source: Facebook
Jihar Kano ta kasance cibiyar siyasar Arewa tun zamanin Jam’iyyar NEPU ta Malam Aminu Kano. A yau, Kano tana cikin wani hali na "rashin tabbas" wanda ya jefa mabiya jam’iyyar NNPP da APC cikin rudani.
Babban abin da ke faruwa a Kano shi ne raɗe-raɗin da ke ƙara ƙarfi cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kusa kammala shirin komawa jam'iyyar APC.
Wannan rahoton ya zo ne bayan kiraye-kirayen ciyamomin Kano ga Abba da Sanata Rabiu Kwankwaso na su ja dukkanin 'yan Kwankwasiyya zuwa APC.
Wani rahoto na jaridar This Day ya nuna cewa Gwamna Abba yana son neman tazarce ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, lamarin da har yanzu ya sanya bai fita daga NNPP ba.
Babbar tambayar ita ce, ko Gwamna Abba zai tafi APC ne tare da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso?
Idan har ya tafi shi kaɗai, hakan na iya alamta rushewar daular siyasar Kwankwasiyya da muka sani tsawon shekaru 20, da ta kafa gwamnatin NNPP a Kano.

Kara karanta wannan
Bashir Ahmad ya soki Abba Kabir kan tsawaita maganar zuwa APC, ya fadi illar dambarwar
A gefe guda kuma, APC a Kano tana fama da nata rikicin; tsakanin tsaffin mabiya Abdullahi Ganduje da kuma magoya bayan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.
Kowannensu na neman iko da jam’iyyar kafin 2027, inda ake rade radin cewa Sanata Barau zai nemi takarar gwamnan jihar ne karkashin APC, cewar rahoton Daily Trust.
2. Jihar Rivers

Source: Facebook
Jihar Rivers ita ce jihar da ta fi kowace jiha rikicin siyasa tun bayan zaɓen 2023, cewar wani rahoto na BBC.
Rikicin siyasa da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon ubangidansa, Nyesom Wike (Ministan Babban Birnin Tarayya), ta wuce gaban wasan kwaikwayo.
Bayan tsawon lokaci ana kai-ruwa-rana, a watan Satumbar 2025, Shugaba Tinubu ya shiga tsakani bayan an dakatar da Fubara na tsawon watanni shida.
Sai dai dawowar Fubara ta zo da sabon lissafi, inda a watan Disamba 2025 ya sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP baki ɗaya.
Wannan mataki ya bar Wike da mambobin majalisar jihar 27 cikin fushi, waɗanda har yanzu suke ƙoƙarin tsige shi ta kowace hanya.
Rikicin Rivers ba kawai na neman iko ba ne; yaƙi ne na mallakar madafun ikon kuɗaɗen jihar da kuma wakilcin yankin Neja-Delta a matakin tarayya.
Duk da sulhun da aka yi a baya, yanzu Rivers tana fuskantar wani sabon zaɓen ƙananan hukumomi wanda ake ganin zai sake rura wutar rikicin, musamman yadda kotun ƙoli ta soke zaɓukan baya.
3. Jihar Legas

Source: Twitter
A Legas, siyasa takan kasance cikin "tsari da lissafi" a ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu. Sai dai a watan Janairu 2025, an samu rikici bayan da ƴan majalisar dokokin jihar suka tsige kakakin majalisa, Mudashiru Obasa.
Ko da yake an dawo da shi daga baya bayan sa-in-sa, hakan ya nuna cewa akwai tsagewa a cikin ginin siyasar APC ta Legas, in ji rahoton Punch.
Akwai jita-jitar cewa wasu ɓangarori na fadar shugaban ƙasa suna son ganin Seyi Tinubu (ɗan shugaban ƙasa) ya fito takarar gwamnan Legas a 2027.
Wannan rahoton ya sanya Gwamna Babajide Sanwo-Olu cikin wani hali na fargaba, kodayake yana kan wa'adinsa na biyu ne dama.
Legas tana fuskantar barazana daga LP wadda ta yi nasara a jihar a babban zaɓen 2023, don haka kowane saɓani a cikin APC na iya zama babban rami ga jam'iyyar.
4. Jihar Kaduna

Source: Twitter
Siyasar Kaduna ta ɗauki sabon salo tun lokacin da Gwamna Uba Sani ya bayyana binciken kuɗaɗen da tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya bari.
Wannan mataki ya juyar da abokantakar shekaru 20 zuwa ƙiyayya ta fili. A yau da muke magana, Nasir El-Rufai baya cikin jam’iyyar APC.
Tsohon gwamnan ya koma ADC, kuma ana ganin yana tattara dukkan tsofaffin makiya da abokan arziki domin ƙaddamar da gagarumar adawa ga gwamnatin Uba Sani a 2027.
Rikicin Kaduna ya fi kowane zafi saboda ana jingina masa kabilanci da addini, inda kowane ɓangare ke amfani da waɗannan katinan don samun karin magoya baya.
5. Jihar Zamfara

Source: Twitter
Zamfara jihar da ke fama da matsalar tsaro, siyasarta ta ta'allaka ne kan wanene zai iya magance ta'addanci. Bayan da Gwamna Lawal Dauda ya doke Bello Matawalle a 2023, fafatawar ba ta ƙare ba.
Matawalle, wanda yanzu minista ne, yana amfani da ikon gwamnatin tarayya wajen gudanar da ayyukan tsaro a jihar, yayin da Lawal Dauda ke zarginsa da "katsalandan".

Kara karanta wannan
Abba da Kwankwaso: Nazari kan abin da ke jawo rikici tsakanin gwamnoni da iyayen gidansu
Wannan gaba ta zama "kashi a wuyan" siyasar Zamfara, inda kusan kowace rana mabiya ɓangarorin biyu ke musayar yawu a gidajen rediyo da kafofin sada zumunta.
Lawal Dauda na ƙoƙarin tabbatar da cewa Matawalle bai sake samun kwarin gwiwar dawowa takara ba, yayin da Matawalle ke gina katanga ta musamman ta hanyar rarraba ayyukan tarayya a jihar.
A hannu daya, kowanne bangare yana zargin juna da hannu a ayyukan ta'addanci, inda har wasu kungiyoyi ke neman Dauda ya yi murabus, shi ma Matawalle ya ajiye mukaminsa.
2027: Jihohin Arewa za su tsaida dan takara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar RAID ta sanar da cewa jihohin Arewa 19 za su sanar da dan takararsu na shugaban kasa a taron da za a yi a Afrilu, 2026.
Babban taron Arewa da za a gudanar zai haɗa kan shugabannin gargajiya da na siyasa domin samar da mafita kan tsaro da ci gaban shiyyar.
Kungiyar ta Arewa ta gargaɗi gwamnati kan rashin hukunta masu laifi da rashin aiwatar da manufofin ilimi waɗanda ke janyo ta'addanci a Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng


