Tsohon IG zai jagoranci kwamitin magance matsalar ta’addanci a Zamfara

Tsohon IG zai jagoranci kwamitin magance matsalar ta’addanci a Zamfara

-Gwamna Bello Matawalle ya kaddamar da kwamiti wanda tsohon babban sifeton yan sanda Mohammed Abubakar zai jagoranta

-An kafa kwamitin ne don kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar

-Abubakar ya yi alkawarin cewa kwamitin na su zai yi aiki tukuru don ganin an magance matsalolin tsaro a jihar

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya kaddamar da kwamiti wanda tsohon babban sifeton yan sanda na Najeriya, Mohammed Abubakar zai jagoranta don magance matsalolin tsaro a jihar.

Haka zalika an baiwa kwamitin alhakin yin bincike kan zanga zangar tashin hankali da aka yi ma sarkin Maru, Alhaji Abubakar Ibrahim da aka dakatar a yan makonnin da suka wuce a bisa zargin cewa da sa hannunsa wajen ta’addancin da a ke fama dashi a jihar.

Gwamnan ya kaddamar da kwamitin jiya Talata 9 ga watan Yuli a gidan gwamnatin jihar dake a Gusau, inda ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne saboda a cimma kudirin gwamnatinshi na ganin ta kawo karshen matsalar tsaro da ake fama dashi a jihar.

Matawalle ya bayyana cewa aikin kwamitin shine ya gano musabbabin ta’addancin da ake fama da shi a jihar da sauran laifuffuka da ake aikatawa a cikin jihar. Ya bayyana cewa tabarbarewar tsaro a jihar ta kai matuka da yanzu mutane ba su iya yin bacci da saleba.

Matawalle ya bayyana cewa sakamakon ta’addancin da ake fama dashi, aikin noma, wanda shine alfaharin yan jihar na neman ya gagaresu.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun yi barna yayin da suka kai farmaki gidan marayu

Kwamitin mai mutane tara ya hada da; sanata Saidu Muhammad Dansadau, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi (Wamban Shinkafi), Jastis Nasir Gummi, Alhaji Mamman Anka, Alhaji Mamuda Maradun da Alhaji Bawa Ibrahim.

Da yake jawabin karbar ragamar jagorancin kwamitin, Abubakar ya bayyana cewa an karramashi da aka bashi wannan jagoranci daga bisani kuma yayi alkawarin cewa za su yi aiki tukuru don ganin sunyi cikakken aikin da aka sanya su su yi.

Ya kara da cewa kwamitin ba zai yi kasa a guiwa ba wajen gayyato kowanne mutum cikin sarakunan gargajiya ko ma’aikatan gwamnati wajen gudanar da aikin su.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel