An Zo Wajen: Kwankwaso Ya Kafa Sharadin Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC
- Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tsokaci kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ba zai dauki magoya bayansa zuwa jam'iyyar APC ba tare da sanin matsayarsa ba
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa a baya sun taimaka wajen kafa gwamnatin APC amma daga baya aka yi watsi da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP a kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan sauya sheka zuwa APC.
Kwankwaso ya bayyana cewa duk wani tunani na shiga APC dole ne ya zo tare da tabbaci karara kan makomar gwamnatin jihar Kano da kuma jin daɗin magoya bayan jam’iyyar.

Source: Twitter
Rabiu Kwankwaso ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 14 ga watan Janairun 2026 a gidansa da ke Miller Road a Kano kamar yadda hadiminsa ya sanya bidiyon a shafinsa na Facebook.
Rabiu Kwankwaso ya gana da magoya baya
Tsohon gwamnan ya yi kalaman ne yayin wani taro da shugabanni da magoya baya daga kananan hukumomin Rano da Dawakin Tofa, tare da wasu kungiyoyin Kwankwasiyya da suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo; kwamishinan kimiyya da fasaha, Yusuf Kofar Mata; dakataccen shugaban jam’iyyar NNPP, Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa; da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar sun halarci taron.
Mahalarta taron sun fito fili sun nuna biyayyarsu ga Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya.
Me Kwankwaso ya ce kan komawa APC?
Kwankwaso ya bayyana cewa dole ne ya san matsayarsa kafin ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
"Ai ba'a tafiya sai ka shirya wadanda za ka tafi da su, sai ka shirya inda za ka tafi. Ba za ka tashi haka kawai ba kana zaune lafiya ka ce kai ka tafi. Ina za ka? To shikenan idan mun shiga mun shirya. Shi ne fa matsalar da ni ake ciki da ni fa."
“Ban ce ba zan shiga APC ba, amma na ce idan zan yi APC, sai an dauko takardun da muka rubuta na me za mu yi wa talakawan Najeriya. Kuma idan zan tafi, sai an gaya min to ni menene matsayina a cikinsu."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Kwankwaso ya tuna baya
Tsohon gwamnan ya tuna da abubuwan da suka faru a baya, inda ya ce mambobin bangarensa sun taimaka wajen kafa gwamnati, amma daga bisani aka yi watsi da su.
“Kowa ya san irin rawar da muka taka suka ce ba sa son mu muka bari. Idan sun canza ra'ayi to me za a yi mana?
"Sannan kuma magoya baya har ma da gwamnatin Kano meye matsayinta? Ai duk sai am fada mun. Har yanzu babu wanda ya zo ya ce mini idan mun tafi me za a ba mu gwamnatin Kano, idan mun tafi za a ba mu 'yan majalisun Kano."
- Rabiu Musa Kwankwaso

Source: Facebook
Madugu bai samu tabbaci a APC ba
An dade ana rade-radin cewa tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya zai rabu da jam'iyyar NNPP ya koma APC.
Kwankwaso ya jaddada cewa har yanzu babu wani tabbaci da aka ba shi da zai tabbatar da cewa zai ci gaba da rike tsarin siyasar jam’iyyar.
“Har zuwa yanzu, babu wanda ya ba ni tabbaci karara cewa za a bar mu, mu ci gaba da rike gwamnatinmu da tsarin siyasar mu. Ina bukatar na san matsayina."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso ya fusata kan Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan shirin Gwamna Abba Kabir na komawa jam'iyyar APC.
Madugun na Kwankwasiyya ya ce ya samu kiraye-kirayen waya game da yadda aka tilasta wa ciyamomi, kansiloli, da zababbun shugabanni sanya hannu kan wata takarda.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya kuma ce ciyamomi, kansiloli da sauran wadanda aka tilasta wa sanya hannu kan takardar da ke neman su goyi bayan Abba ya shiga APC, sun shiga mawuyacin hali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


