Kwankwaso Ya Fusata game da yadda Abba Ke Tilasta wa Ciyamomin Kano Binsa APC
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin Kano da tilasta wa ciyamomi zaba tsakanin Kwankwasiyya da Gandujiyya a jihar
- Rikici ya kazance tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba K. Yusuf biyo bayan rahotannin shirin gwamnan na komawa jam'iyyar APC
- A cikin wani bidiyo, jagoran Kwankwasiyyar ya fadi halin da ciyamomi da zababbun shugabanni suka shiga kan batun sauya shekar Abba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya da jam'iyyar NNPP, ya yi magana game da batun sauya shekar Abba Yusuf, gwamnan Kano zuwa APC.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce ya samu kiraye-kirayen waya game da yadda aka tilasta wa ciyamomi, kansiloli, da zababbun shugabanni sanya hannu kan wata takarda.

Source: Facebook
'Ana tilasta wa ciyamomin Kano' - Kwankwaso
A cikin wani bidiyo da Hon Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ji Kwankwaso ya warware dukkan tirka-tirkar siyasar da ke faruwa a Kano.
Kwankwaso ya ce ya tarar da wani abu marar dadi da yake faruwa a Kano, inda gwamnatin Abba Yusuf ta ke tilasta ciyamomi, kansiloli su zabi Gandujiyya ko Kwankwasiyya.
Kwankwaso, a cikin bidiyon ya ce:
"'Yau 13 ga watan 1, shekara ta 2026, na shigo nan jiha ta mu mai albarka, jihar Kano, kuma na samu abubuwan jin dadi masu yawa, wasu kuma babu dadi, musamman yadda gwamnati ta fito da wani tsari na takurawa ciyamomi, kansiloli, sakatarori, da sauran mutane masu rikon mukami."
Ya ce an takura wa wadannan zababbu ne, "da nufin cewar su rubuta sunansu, wa suke so, Kwankwasiyya suke so ko Gandujiyya."
Kwankwaso ya nuna cewa:
"Wannan abu ne wanda yake marar dadi, wanda duk wani masoyi, ba ma namu kadai ba, na jihar Kano, ba zai ji dadi ba."
Kwankwaso ya tabo batun butulci a siyasa
Tsohon gwamnan Kano, ya kuma tabo batun siyasar jihar, da yadda ya ce ya fuskanci butulci a 2015, amma a karshe, Allah ya ci gaba da daukaka tafiyar Kwankwasiyya.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce:
"Mun duba wadannan abubuwa, mun duba tarihi, mun ga yadda abubuwa suka taso, musamman a wannan tafiya ta mu, mun ga abubuwan da suka faru musamman a 2015, musamman na butulci da muka samu, magoya bayanmu suka sha wahala na shekara takwas."

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An bayyana abin da ya jawo sabani tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba
Kwankwaso ya ce duk da wahalar da magoya bayan Kwankwasiyya suka sha, sun yi tawakkali, sun yi hakuri, har aka je shekarar 2019 da 2023 inda jama'a suka zabi NNPP.

Source: Facebook
Halin da ciyamomi suka shiga kan shirin Abba
Sanata Kwankwaso ya kuma ce ciyamomi, kansiloli da sauran wadanda aka tilasta wa sanya hannu kan takardar da ke neman su goyi bayan Abba ya shiga APC, sun shiga mawuyacin hali.
Ya ce ya samu kira daga ciyamomi da wadanda ke iya yi masa magana, game da wannan batu, kuma har ma an kara ma wasu ruwa saboda tsananin damuwar da suka shiga.
"Wasu ba sa barci, wasu sun shiga dimuwa, wasu an kara masu ruwa a asibiti."
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Mabiya Kwankwaso sun ki zuwa taron Abba
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu 'yan siyasa masu biyayya ga Rabiu Musa Kwankwaso ba su halarci taron da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya a Kano ba.
Taron raba tallafi a Kano shi ne fitowar gwamnan na farko bainar jama'a tun bayan fara rade-radin sauya sheƙarsa daga NNPP mai-ci zuwa APC.
Rashin zuwan manyan masu yi wa Kwankwaso biyayya taron ya ƙara tayar da jita-jita game da rikicin siyasa a Kano, musamman a Kwankwasiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
