Kwankwaso Ya Fadawa Ciyamomin Kano abin da Za Su Yi a Shirin Abba na Shiga APC

Kwankwaso Ya Fadawa Ciyamomin Kano abin da Za Su Yi a Shirin Abba na Shiga APC

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ba ciyamomin Kano shawarar sanya hannu kan takardar goyon bayan sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa da yawa daga cikin masu rike da mukamai sun shiga mawuyacin hali har da kwanciya a asibiti saboda rigimar
  • Jagoran na NNPP ya jaddada cewa masoyansa na nan daram suna jiran zaben 2027 domin nuna karfin Kwankwasiyya a Kano da kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya da jam'iyyar NNPP, ya ba ciyamomi, kansiloli da masu mukamai a Kano shawara su bi Gwamna Abba Yusuf zuwa APC.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce ya samu kiraye-kirayen waya game da yadda gwamnatin Kano ke tilasta zababbun shugabannin su sanya hannu kan wata takarda.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Fusata game da yadda Abba Ke Tilasta wa Ciyamomin Kano Binsa APC

Sanata Rabiu Kwankwaso ya amince zababbu shugabannin Kano su bi gwamna zuwa APC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zaune tare da Gwamna Abba Yusuf da gangamin Kwankwasiyya. Hoto: @Kyusufabba
Source: Facebook

Tirka-tirkar sauya shekar Abba a Kano

A cikin wani bidiyo da Hon Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya tariyo irin gwagwarmayar da aka sha, har aka kafa gwamnatin Abba, da abin da ke faruwa yanzu.

Wannan jawabi da Kwankwaso ya yi, martani ne ga wani shiri na gwamnan Kano, Abba Yusuf na shirin sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC kamar yadda aka rahoto.

Kano ta shiga shekarar 2026 da jita-jitar sauya shekar Abba, da kuma yadda aka ji kungiyar ciyamomin Kano tana umartar mambobinta su jagoranci tarukan kiran Abba da Kwankwaso su jagorance su zuwa APC.

An samu ce-ce-ku-ce sosai kan wannan batu, inda har yanzu ba a ji ta bakin gwamnan a hukumance ba, amma har an samu bayanai na ranar da aka shirya zai shiga APC, da kuma martanin jam'iyyar APC.

Kwankwaso ya fadi halin da ciyamomi ke ciki

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An bayyana abin da ya jawo sabani tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

A cikin wannan sabon bidiyo, Kwankwaso ya nuna takaicinsa kan yadda aka rika tilasta ciyamomin su sanya hannu kan takardar zabar Kwankwasiyya ko Gandujiyya kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Legit Hausa ta rahoto cewa Kwankwaso ya ce tun da rigima ta taso a Kano, na a tafi a koma wajen Ganduje da Bola Tinubu, mutane ke ta fama da bacin rai da rigingimu.

"Ciyamomi da yawa sun bugo mun waya, kansiloli da sauran masu rike da mukamai, da 'yan majalisar jaha, wasu sun yi mun magana, kan halin da suke ciki.
"Wasu ba sa barci, wasu sun shiga cikin dimuwa, wasu an kakkara masu ruwa a asibiti. Wannan na tuntubi mutane wadanda nake ganin ya dace, domin a sama masu sauki."

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce ya amince ciyamomi su bi Abba zuwa APC don nema masu sauki.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya na gabatar da jawabi a wani tare, a kusa da shi akwai Gwamna Abba Yusuf. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Kwankwaso ya amince ciyamomi su bi Abba

Sanata Kwankwaso ya ce har yanzu akwai hakkinsu a hannun gwamnati, don haka daukar wani mataki sabanin abin da ke faruwa zai iya jefa mutane a mawuyacin hali.

"Shi ne muka ga ya dace, duka ciyamomi, da kansiloli, da zababbu, da kansilolin sa ido, da dukkan wanda aka je aka ce ya sa hannu, mu ba mu da matsala ya sa hannu."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta zabi na zaba tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso ya ce suna sane cewa har yanzu ma ba a fara rigimar siyasar shekarar 2027 ba, don haka, suna nan suna jira da masoyansu don jiran wannan zabe.

Ya kara da cewa:

"Masoyanmu suna nan, duk inda suke, sun san kansu, mun san su, kuma wannan zai ba da dama, wadanda aka takurawa, su samu saukin halin da suke ciki."

Kwankwaso ya kuma godewa Abba, kan yabawa gwamnatinsa, da kuma tona asirin gwamnatin Ganduje da ya ce ta dakatar da ayyukan ci gaba a Kano.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Kwankwaso na fuskantar babbar matsala a siyasa

A wani labari, mun ruwaito cewa, farin jinin jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Injiniya Rabiu Kwankwaso da mabiyansa ya fara dusashewa a siyasar jihar Kano.

Kungiyar KPRA ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da shugabanta, Isyaku Lawal Tofa ya fitar kan kan rade-radin sauya shekar gwamnan Kano.

KPRA ta yi kira ga mambobin jam'iyyar NNPP da mabiyan Kwankwaso su zauna su yi tunani kan irin siyasar da maigidansu ke yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com