Magana Ta Fito: An Bayyana Abin da Ya Jawo Sabani tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba
- Alamu sun nuna cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ubangidansa a siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Hakan na zuwa ne yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ci gaba da shirin sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki a Najeriya
- Wata majiya ta bayyana cewa buri na siyasa ya taka rawar gani wajen kawo sabani tsakanin madugun Kwankwasiyya da Gwamna Abba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - An samu rarrabuwar kai tsakanin Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
An bayyana cewa hakan ya auku ne sakamakon rikicin da ya shafi zaben gwamna na shekarar 2027 da ake tunkara.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce wata majiya ta bayyana mata dalilin da ya kawo rarrabuwar kai tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Me ya hada Gwamna Abba da Kwankwaso?
Majiyar ta bayyana cewa gwamnan zai fice daga NNPP zuwa jam’iyyar APC ne domin cimma burinsa na sake tsayawa takarar gwamna karo na biyu.
A cewar majiyar, rikici mai tsanani ya dade yana gudana tsakanin gwamnan da jagoran na jam’iyyar NNPP, saboda Kwankwaso bai nuna shirin mara wa Gwamna Abba baya don samun wa’adi na biyu ba.
Majiyar ta kara da cewa, duk da cewa Gwamna Abba surikin Kwankwaso ne, gwamnan ya sha korafi kan abin da yake kira tsoma baki fiye da kima a harkokin mulki da siyasa.
Me ya ja hankalin Gwamna Abba zuwa APC?
An ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yanke shawarar komawa APC ne saboda a can zai zama jagoran jam’iyyar APC a Kano kai tsaye.
Hakazalika kuma komawarsa APC za ta ba shi damar samun babbar dama ta tsayawa takara da kuma lashe tikitin gwamna a 2027.
“Gwamnan Kano ya yanke shawarar barin NNPP ne domin idan ya zauna a can, makomarsa ta siyasa za ta kare a 2027. An riga an sanar da mataimakin gwamna ya fara shirin da ya dace.”
- Wata majiya

Source: Facebook
Magoya bayan Abba na son ya yi tazarce
Majiyar ta kara da cewa magoya bayan Gwamna Abba na ganin cewa gwamnan ya yi aiki tukuru kuma ya cancanci samun tikitin wa’adi na biyu, amma ana shirin hana shi hakan.
“Kwankwaso da magajinsa, Abdullahi Umar Ganduje, sun yi wa’adi na shekara takwas kowannensu. Gwamnan Kano kuma yana da cikakken goyon bayan majalisar dokokin jihar."
“Gwamna Abba Kabir Yusuf yana shirin shiga jam’iyyar da ke mulki ne domin ya haɗa karfinsa da ikon gwamnatin tarayya, domin ci gaba da rike Kano. Wannan babban rashi ne ga NNPP da kuma jagoranta."
- Wata majiya
NNPP ta goyi bayan Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta tsoma baki a takaddamar da ke tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam'iyyar mai mulki a jihar Kano rak ta bayyana cewa tana goyon duk wani matakin siyasa da Gwamna Abba zai dauka a rikicinsa da Kwankwaso.
Shugaban wani tsagi na NNPP, Agbo Major ya bayyana cewa bai kamata Kwankwaso ya yi adawa da shirin Gwamna Abba na komawa APC ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

