Jam'iyyar NNPP Ta Zabi na Zaba tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

Jam'iyyar NNPP Ta Zabi na Zaba tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba

  • Ana ci gaba da maganganu kan batun sauya shekar Gwamnan Kano wato Alhaji Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
  • Tsagin jam'iyyar NNPP ya fito ta nuna goyon bayanta ga gwamnan kan rikicin siyasa da ke tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Agbo Major wanda ke shugabantar tsagin NNPP ya bayyana cewa bai kamata Kwankwaso ya yi zargin Gwamna Abba ya ci amanarsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP ta yi tsokaci kan takaddamar siyasa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

NNPP ce tana goyon bayan duk wani matakin siyasa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, zai ɗauka a rikicin da ke tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamna Abba ya samu goyon baya daga wajen NNPP
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Agbo Major, ya fitar.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: 'Dan Kwankwaso ya zabi wanda zai bi tsakanin mahaifinsa da Gwamna Abba

NNPP ta goyi bayan Abba Kabir Yusuf

NNPP ta bayyana cewa Gwamna Abba, a matsayinsa na gwamna daya tilo kuma jagoran jam’iyyar, yana bukatar cikakken goyon bayan jam’iyyar domin ya samu nasara a Kano.

“Ko shakka babu Kwankwaso ya taka rawa wajen taimaka wa Abba ya zama gwamna, amma a matsayinsa na gwamna, ya kamata a bar shi ya yi aiki, ya yi nasara, ba tare da shagala da siyasar son kai da ba ta da amfani ba."

- Agbo Major

Jam'iyyar NNPP ta ragargaji Rabiu Kwankwaso

Agbo Major ya ce jihar Kano na da matukar muhimmanci ba kawai a zaben 2027 ba, har ma ga NNPP baki ɗaya, don haka jam’iyyar ba za ta bari Kwankwaso da kungiyar Kwankwasiyya su ci gaba da tsoma baki har su lalata abin da ta samu a jihar ba.

“Kwankwaso shi ne ɗan takararmu na shugaban kasa a 2023, amma daga baya an kore shi daga jam’iyya bisa zargin aikata ayyukan adawa da jam’iyya."

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya nemi a biya su da Gwamna Abba ya karbi katin shiga APC

"Bai kamata dangantakarsa ta kashin kai da gwamnan ta shafi harkokin mulkin Kano ko kuma jam’iyyar siyasar da gwamnan zai zaɓa ba."

- Agbo Major

'Kwankwaso ya ci amanarmu' - Jam'iyyar NNPP

NNPP ta bayyana lamarin a matsayin abin mamaki yadda Kwankwaso, wanda a cewarta ya ci amanar wanda ya kafa NNPP, Dr. Boniface Aniebonam, yanzu yake kuka da zargin cewa gwamnan Kano ya ci amanarsa.

Agbo Major ya zargi Kwankwaso da kokarin kwace jam’iyyar bayan zaben 2023, bayan wa’adin yarjejeniyar fahimta tsakaninsa da NNPP da kuma Kungiyar Kwankwasiyya ta kare, jaridar The Nation ta kawo labarin.

“Kararrakin da Kwankwaso ya shigar ne suka haddasa ficewar mambobin jam’iyyarmu da yawa a Kano zuwa wasu jam’iyyun siyasa."
“Ba za mu zauna muna kallo Kwankwaso yana ci gaba da lalata sunan gwamnan Kano ta hanyar furuci da barazana ba.”

- Agbo Major

Ya kuma shawarci Kwankwaso da ya koyi darasi daga jam’iyyar APC, wadda ke bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu dama da goyon baya ya yi aiki ba tare da tursasawa ko tsoma baki ba.

Kara karanta wannan

"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba

Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin komawa jam'iyyar APC
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

NNPP na so Abba ya ci gaba da zama a cikinta

Agbo Major ya kara da cewa NNPP ta yi asarar tasirinta a siyasa kuma ta kasa shiga wasu zabubbuka a baya sakamakon abin da ya kira mummunan halin Kwankwaso.

“Saboda haka, a wannan yanayi, a fili yake cewa burin gwamnan jihar Kano na sauya sheka zuwa APC abin fahimta ne kuma mai ma’ana."
“Duk da haka, matsayar jam’iyyarmu ita ce Gwamna Abba Kabir Yusuf kada ya bar NNPP, sai dai ya ɗauki nauyin jagorantar jam’iyyar, ya kuma tura ta zuwa manyan nasarori a gaba."

- Agbo Major

Gwamna Abba ya kammala shirin shiga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa alamu sun nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya kammala shirin komawa jam'iyyar APC.

Wata majiya daga majalisar zartarwar jihar Kano ta tabbatar da cewa an kammala dukkan matakan shirye-shirye.

Hakazalika, majiyar ta ce jam’iyyar APC a jihar Kano ta shiga yanayin shirin tarbar Gwamna Abba tare da magoya bayansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng