An Zo Wajen: Shugaban PDP Ya Tsage Gaskiya kan Batun Sauya Shekar Gwamna Bala zuwa ADC

An Zo Wajen: Shugaban PDP Ya Tsage Gaskiya kan Batun Sauya Shekar Gwamna Bala zuwa ADC

  • Ana ta yada jita-jita kan cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed na shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa ADC
  • Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Bauchi, Hon Sama'ila Adamu Burga, ya yi tsokaci kan batun sauya shekar Gwamna Bala zuwa ADC
  • Ya bayyana cewa Gwamna Bala bai da wata niyya ta barin jam'iyyarsa ta PDP zuwa wata jam'iyya ta siyasa daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Jam’iyyar PDP a jihar Bauchi ta yi martani kan jita-jitar cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin sauya sheka zuwa ADC.

Jam'iyyar PDP ta yi watsi da abin da ta kira rahotannin karya da yaudara da ke zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin ficewa daga PDP zuwa ADC.

Gwamna Bala Mohammed zai ci gaba da zama a PDP
Gwamna Bala Mohammed a wajen taron jam'iyyar PDP Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban PDP a Bauchi, Hon. Sama'ila Adamu Burga ya fitar ranar Juma’a, 9 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

An kira sunan Atiku da aka lissafa 'yan siyasar da suka 'ruguza' jam'iyyar PDP

Me PDP ta ce kan sauya-shekar Gwamna Bala?

Jam’iyyar ta bayyana rahoton a matsayin kirkirarre, marar tushe, tana kuma kira ga jama’a da su yi watsi da abin da ta kira yaɗa ƙarya da gangan da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu kafafe marasa sahihanci.

Hon. Sama’ila Adamu Burga ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed ba shi da wata niyya ko kaɗan ta barin PDP zuwa ADC ko wata jam’iyya daban.

A cewar Burga, an riga an karyata wannan jita-jita gaba ɗaya a wani babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar ranar Lahadi, 4 ga Janairu, 2026, wanda Gwamna Bala Mohammed da kansa ya karɓi bakuncinsa.

Manyan PDP sun gana da Gwamnan Bauchi

A yayin taron, shugabannin jam’iyyar da manyan masu ruwa da tsaki sun sabunta mubaya’arsu ga PDP tare da kaɗa kuri’ar amincewa baki ɗaya ga Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed.

Ya ce taron ya samu halartar manyan shugabannin jam’iyyar, ciki har da mataimakin shugaban PDP na kasa, ‘yan majalisar dokokin jihar Bauchi karkashin jagorancin kakakin majalisa.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya nemi a biya su da Gwamna Abba ya karbi katin shiga APC

Sauran su ne mambobin majalisar zartarwa ta jihar, shugabannin jam’iyyar na jiha da kananan hukumomi, shugabannin kananan hukumomi 20 da aka zaɓa, ‘yan majalisar wakilai masu ci, tsofaffin sanatoci da sauran manyan jiga-jigan siyasa daga faɗin jihar.

Shugaban PDP ya kuma bayyana cewa Gwamna Mohammed ya nuna matuƙar godiya bisa ƙuri’ar amincewar da aka ba shi, tare da jaddada cikakkiyar biyayyarsa ga PDP.

Gwamna Bala zai ci gaba da zama a PDP

Burga ya jaddada cewa gwamnan ba ya yanke manyan shawarwarin siyasa shi kaɗai, yana mai cewa tattaunawa, haɗin kai da jagoranci na bai ɗaya su ne ginshiƙan PDP.

“A kowane lokaci, ko a ɓoye ko a fili, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed bai taɓa bayyana wata niyya ta sauya sheƙa zuwa ADC, APC ko wata jam’iyya ba."

- Hon. Sama'ila Adamu Burga

Gwamna Bala Mohammed zai ci gaba da zama a PDP
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Ya kara da cewa PDP a shirye take ta yi hulɗa mai ma’ana da sauran jam’iyyun siyasa domin kwanciyar hankali da karfafa dimokuraɗiyya a kasa.

Sai dai, ya ce irin wannan hulɗa dole ne ta kasance bisa gaskiya, mutunta juna da ka’idojin dimokuraɗiyya, ba bisa jita-jita da kirkira ba.

Burga ya kammala da cewa Gwamna Bala Mohammed na nan daram a PDP, a matsayin shugaba mai biyayya, jajircewa kan manufofi, wanda ya tsaya tsayin daka kan akidun jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: CAN ta magantu kan Gwamna Bala bayan shafa masa kashin kaji

EFCC ta yi wa Gwamna Bala martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta yi martani ga Gwamna Bala Mohammed kan zarge-zargen da ya yi a kanta.

Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Bala ya yi zargin cewa abokan hamayyarsa na siyasa na amfani da hukumar wajen muzguna ma shi da jami’an gwamnatinsa.

EFCC ta ce abin raini ne gwamnan ya danganta ayyukan hukumar a Bauchi da tasirin wani mai rike da mukamin siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng