Siyasar Kano: 'Dan Kwankwaso Ya Zabi Wanda da Zai Bi tsakanin Mahaifinsa da Gwamna Abba
- Alamu sun nuna cewa wasu daga cikin kwamishinonin gwamnatin Kano za su yi murabus idan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC
- Majiyoyi sun bayyana cewa 'dan Rabiu Kwankwaso, Mustapha ya fara shirye-shiryen ajiye aiki kafin ko bayan Abba Gida-Gida ya bar NNPP
- Rahoto ya nuna cewa duk da wasu kwamishinoni sun nuna cewa suna tare da Kwankwaso, Abba ya ja tawaga mafi rinjaye a majalisar zartawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Kwamishinan matasa da wasanni na Kano, Mustapha Kwankwaso na shirin barin mukaminsa gabanin sauyin sheƙar Gwamna Abba Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Mustapha shi ne babban ɗan tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam'iyyar NNPP kuma tsohon dan takarar shugaban kasa.

Source: Twitter
Premium Times ta ce duk da Mustapha bai mika takardar murabus a hukumance ba, kuma gwamnan bai cire shi daga mukaminsa ba, majiyoyi sun ce zai yi murabus a kafin ko bayan Abba ya bar NNPP.

Kara karanta wannan
"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba
Dalilin Gwamna Abba na komawa APC
Ko da Gwamna Abba bai bayyana a fili cewa zai fice daga NNPP ba, mataimakansa da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar sun tabbatar da shirinsa na komawa APC.
Sun danganta hakan da rikice-rikicen shari’a da ke kara tsananta a cikin NNPP, wanda ya sa suke gudun abin da ya faru da APC a Zamfara, ya faru a Kano.
Shin dan Kwankwaso zai bi Abba zuwa APC?
Majiyoyi sun shaida wa jaridar cewa Mustapha Kwankwaso ya bar ma’aikatarsa tare da kwashe kayansa bayan mahaifinsa, ya nuna rashin amincewa da shirin gwamnan na sauya sheƙa.
Zuwa yau Juma'a, manyan jiga-jigai da masu rike da mukamai da dama sun sake jaddada mubaya'arsu ga Kwankwaso, tare da tabbatar da ba za su bi gwamnan zuwa APC.
Daga cikinsu akwai Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Yusuf Kofar-Mata; Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai, Adamu Aliyu; Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Ibrahim Umar da Kwamishinan Albarkatun Ma’adanai, Hamza Kachako.

Kara karanta wannan
Mataimakin shugaban NNPP ya tono wata doka, ya dora Gwamna Abba a saman Kwankwaso
Sauran da aka ruwaito sun sanya hannu a rajistar mubaya'a ga Kwankwaso sun hada da Shugaban Ma’aikatan Kano, Abdullahi Musa; Shugaban Hukumar Tallafin Karatu, Musa Danzaki; da shugaban kasuwar Kwari, Hamisu Dogonnama.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya samu rinjaye a NNPP
Amma duk da haka, bayanai sun nuna cewa Gwamma Abba ya samu rinjaye daga cikin yan Majalisar tarayya da na jiha, kamar yadda Leadership ta kawo.
An ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir ya samu rinjayen masu goyon baya a cikin masu rike da mukamai, a abin da majiyoyi suka bayyana a matsayin “juyin mulki na cikin gida”.
Dukkan shugabannin kananan hukumomi 44, mataimakansu, da mafi yawan shugabannin mazabu sun bi gwamnan a shirin sauya sheƙa zuwa APC.
Kwankwaso ya soki shirin Gwamna Abba
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf kan shirin komawa jam'iyyar APC, inda ya bayyana hakan da 'cin amana'.
Kwankwaso ya gargaɗi waɗanda ke shirin bin Gwamna Abba zuwa APC cewa lallai akwai sakamako ga duk wanda ya ci amanar tafiyar da ta gina shi.
Tsohon gwamnan na Kano ya bukaci dukkan mambobin NNPP da ke son sauya sheka zuwa APC da su biya diyya ga tafiyar Kwankwasiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng