'Yan Majalisa 2 Sun Fice daga Jam'iyyar PDP, Sun Gana da Shugaban Gwamnonin Arewa
- Jam'iyyar APC ta kara mamaye Majalisar dokokin jihar Gombe bayan mambobi biyu sun tabbatar da ficewarsu daga PDP
- 'Yan Majalisar sun sanar da komawa APC mai mulki domin samun cikakken damar tallafawa manufofin ci gaba na gwamnatin Gombe
- Gwamna Inuwa Yahaya ya ce wannan sauya sheka ta nuna yadda jama'a suka gamsu tare da aminta da gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Wasu mambobi biyu na Majalisar Dokokin Jihar Gombe daga jam’iyyar adawa ta PDP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
’Yan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Gabriel Galadima Fushison, mai wakiltar Kaltungo ta Yamma, da kuma Malon Nimrod Yari, mai wakiltar Shongom.

Source: Facebook
'Yan Majalisa 2 sun koma APC a Gombe
Premium Times ta ce sun sanar da ficewarsu a hukumance ne a ranar Laraba, sannan daga bisani suka kai ziyara fadar gwamnatin Gombe inda suka gana da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Rt. Hon. bubakar Mohammed Luggerewo, ne ya jagoranci tawagar zuwa fadar gwamnati tare da mataimakinsa, Sadam Bello da sauran shugabannin majalisar.
Dalilan sauya shekar 'yan Majalisa 2
A cewar ’yan majalisar, sun yanke shawarar sauya sheƙa ne sakamakon tsarin shugabanci na haɗin kai, nagarta da kuma kyakkyawan aiki da Gwamna Inuwa Yahaya ke yi tun bayan hawansa mulki.
Sun bayyana cewa ko da suna PDP, hakan bai hana su kyakkyawar mu’amala da bangaren zartarwa ba, inda suka ce mutanen mazabunsu sun amfana da ayyuka da shirye-shiryen gwamnatin jihar.
“Abin da ya sa muka yanke wannan shawara shi ne adalci, nagartaccen shugabanci da kuma jajircewar gwamna wajen tabbatar da ci gaba a faɗin jihar,” in ji ’yan majalisar.
Sun ƙara da cewa shiga APC zai ba su damar tallafa wa manufofin ci gaba na gwamnatin jihar Gombe yadda ya kamata.
Abin da Gwamna Inuwa ya fada masu
Da yake karɓar su cikin APC, Gwamna Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban gwamnonin Arewa, ya ce sauya shekar ta nuna yadda jama'a suka aminta da gwamnatinsa.
Ya ba su tabbacin cewa za a ba su cikakken matsayi da kulawa iri ɗaya da sauran mambobin jam’iyyar, kamar yadda jaridar People Gazette Nigeria ta ruwaito.
Gwamnan ya kuma yaba wa shugabancin Majalisar Dokokin jihar bisa kyakkyawar fahimta da haɗin kai da bangaren zartarwa, yana mai cewa hakan ne ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gombe.

Source: Twitter
Ya nuna ƙwarin gwiwar cewa haɗin kai a cikin APC zai kai jam’iyyar ga nasara a zaɓen 2027 a jihar Gombe da ma ƙasa baki ɗaya.
Da wannan sabon ci gaba, jam’iyyar APC yanzu tana da kujeru 23 cikin 24 na Majalisar Dokokin Jihar Gombe, yayin da PDP ta rage da ɗan majalisa guda ɗaya kacal.
Tsohon gwamnan Abia ya koma APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan na jihar Abia, Sanata Theodore Orji, ya sanar da dawowa siyasa gadan-gadan, tare da bayyana ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Ana ganin cewa tsohon gwamnan ya na ɗaya daga cikin manyan ginshikan jam’iyyar PDP masu tallafa mata a jihar Abia, kuma komawarsa APC na iya rusa tsarinta gaba daya.
Mai ba tsohon gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Mista Ifeanyi Umere, ya ce maigidansa ya yanke wannan shawara ne bisa ra'ayin kansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

