Ministan Tinubu Zai Tsaya Takarar Gwamnan Neja a 2027? Mohammed Idris Ya Magantu
- Ministan yada labarai Mohammed Idris ya karyata rahotannin dake cewa zai shiga yakin neman takarar gwamnan Neja a zaben 2027
- Alhaji Mohammed Idris ya dakatar da hadiminsa, Sa’idu Enagi wanda shi ne ya wallafa rubutun da ke yawo game da batun takararsa
- A wata sanarwa da ministan ya wallafa a shafukansa na sadarwa, ya bayyana irin alakar da ke tsakaninsa da Gwamna Umaru Bago
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan yaɗa labarai da wayar da kai na kasa, Alhaji Mohammed Idris (wanda aka fi sani da Malagi), ya fito fili ya yi magana game da batun tsayawa takararsa a 2027.
Idris ya nesanta kansa da wani rubutun siyasa da ke yawo a kafafen yaɗa labarai mai taken “Malagi 2027,” da hadiminsa, Sa'idu Enagi ya wallafa.

Source: Twitter
Minista ya nesanta kansa da batun takarar gwamna
Wannan rubutu dai ya yi hasashen yiwuwar sauye-sauyen siyasa da kuma shirye-shiryen takarar gwamnan jihar Neja a zaɓe mai zuwa na shekarar 2027, in ji rahoton jaridar Vanguard.
A wata sanarwa, ta nesanta Idris da wannan rubutu da ofishin ministan ya fitar ranar Laraba, 7 ga Janairu, 2026, an bayyana cewa wannan rubutu an yi shi ne ba tare da izini ko amincewar ministan ba.
Sanarwar da Idris ya wallafa a shafinsa na X, ta fayyace cewa ɗaya daga cikin hadiman ministan, mai suna Sa’idu Enagi, ne ya wallafa rubutun a kashin kansa.
Ministan ya nanata cewa ra’ayoyin da aka bayyana a rubutun ba su wakiltar matsayinsa ko manufofinsa na siyasa, don haka ya yi kira ga daukacin jama’a da su yi watsi da wannan rubutu gaba ɗaya.
Ministan labarai ya kori hadiminsa
A cewar ministan, a halin yanzu hankalinsa ya karkata ne kacokan kan nauyin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗora masa na tafiyar da ma’aikatar yaɗa labarai ta tarayya.
Sakamakon hakan, Ministan ya ba da umarnin gudanar da bincike na gaggawa kan yadda aka yi rubutun, yayin da sanarwar ta ce:
"Ana rokon jama'a da su yi watsi da wannan rubutu domin ministan bai ba da umarnin a yi ba, kuma ba da amincewarsa aka wallafa shi ba.
"Hakazalika, ministan ya ba da umarnin gudanar da binciken gaggawa, sannan an mika takardar dakatarwa ta nan take ga hadimin da ya yi wannan rubutu."

Source: UGC
Alakar minista da Gwamnan Neja
Haka kuma, sanarwar ta nuna kyakkyawar alaƙar aiki da ke tsakanin ministan labarai, Mohammed Idris da gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago.
Sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun ministan, Rabiu Ibrahim, ta bayyana cewa shugabannin biyu suna aiki tare domin tabbatar da tsaro da ci gaban jihar Neja.
Ministan ya yi gargaɗi cewa duk wani hasashen zaɓen 2027 a yanzu zai zama cikas ga waɗannan manyan manufofi na ci gaba da aka sanya a gaba.
Alhaji Mohammed Idris, wanda ya kasance babban mai neman takarar gwamna a APC a shekarar 2023, ya jaddada cewa babban burinsa a yanzu shi ne tabbatar da nasarar manufofin gwamnatin Tinubu.
Minista ya samawa 'yan jiharsa ayyuka
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce ya samar da guraben aiki na tarayya guda 30 ga ‘yan asalin jihar Neja,
Ministan ya ce ya yi wasu manyan ayyuka a garinsa Malagi, ciki har da gina makarantar Islamiyya, masallatai, da aikin wutar lantarki.
Mohammed Idris ya jaddadawa al'umma cewa manufofin shugaba Bola Ahmed Tinubu za su samar da ci gaba mai dorewa ga Najeriya.
Asali: Legit.ng


