An Fadi Shekarun da Mulki zai Yi a Kudu kafin Ya Dawo Yankin Arewa
- Jagoran Obedient Movement, Dr. Yunusa Tanko, ya ce Peter Obi babban mai burin takara ne a zaben 2027 kuma ba zai zama mataimaki ga kowa ba a ADC
- Yunusa Tanko ya jaddada alkawarin Obi na yin wa’adi daya kacal idan ya yi nasara, inda ya ce zai kammala mulki sannan ya mika mulki ga Arewa
- Ya bayyana cewa shigar Obi jam'iyyar ADC ta biyo bayan tuntubar jama’a da kungiyoyi daban-daban, ba don son rai ko matsin siyasa da aka yi masa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban Obedient Movement, Dr. Yunusa Tanko, ya sake jaddada cewa Peter Obi na daga cikin manyan ’yan takarar kujerar shugaban kasa a 2027.
Ya yi magana yana mai cewa tsohon dan takarar LP ba zai amince ya zama mataimakin wani dan siyasa ba a jam’iyyar ADC.

Source: Twitter
Yunusa Tanko ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Frontline na tashar Eagle 102.5 FM, inda ya ce wannan matsaya na nuna gaskiya da kishin hadin kan kasa.
Mulki zai dawo hannun Arewa a 2031
A cewar Tanko, alkawarin Obi na wa’adi daya ba ga wata jam’iyya kadai ba ne, illa alkawari ne da ya yi wa ’yan Najeriya gaba daya.
Ya ce idan aka zabe shi a 2027, Obi zai cika ragowar wa’adin Kudu na shekaru hudu sannan ya mayar da mulki ga Arewa a 2031, lamarin da ya ce zai taimaka wajen karfafa amana da zaman lafiya a kasa.
Yunusa Tanko ya ce wannan matsaya ta nuna cewa Peter Obi na da gaskiya da hangen nesa domin cigaba da hada kan kasa baki daya.
Jam'iyyar ADC da rade-radin tasirin Atiku
Da yake mayar da martani kan rade-radin cewa ADC na karkashin tasirin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Tanko ya yi watsi da hakan.
Ya ce dukkan wadanda suka hada wannan kawance sun bayar da gudunmawa da kudinsu, kuma babu wanda ya mallaki jam’iyyar shi kadai.
Ya ce hankalinsa yana kan dan takararsa ne kawai, inda yake gabatar da Obi ga jama’a bisa cancanta, kwarewa, da abin da zai iya bai wa Najeriya, ba wai bisa alakoki na siyasa ba.
Dalilin shigar Peter Obi ADC
Yunusa Tanko ya tabbatar da cewa Peter Obi, tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a 2023, ya shiga ADC a hukumance domin ceto Najeriya.
Ya ce wannan mataki ya biyo bayan tuntuba mai fadi da kungiyoyi da jama’a daban-daban da ke son a gyara matsalolin kasar.
Game da manufofi, The Guardian ta rahoto Yunusa Tanko ya ce idan Obi ya hau mulki, zai mayar da hankali kan daidaita tattalin arziki, tsaron kasa, da zuba jari a harkar noma.

Source: Facebook
Venezuela: ADC ta yi kira ga Bola Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta ragargaji gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan yin shiru bayan kama shugaban Venezuela, Nicolas Maduro.
ADC ta ce abin kunya ne a ce Najeriya ta gaza magana a kan babban lamari da ya shafi duniya a lokacin da kasashe ke bayyana matsayarsu.
Shugaban Amurka, Donald Trump ne ya tura sojoji kasar Venezuela suka kama Nicolas Maduro bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


