Rikicin PDP: An Ji Abin da Jonathan Ya Fadawa Shugabannin Jam'iyyar a Abuja
- Jam’iyyar PDP ta kai rikicin shugabanci wajen tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a babban birnin tarayya na Abuja
- Shugaban PDP, Taminu Turaki ya ce Jonathan ya tabbatar har yanzu cikakken mamba ne na jam'iyyar, kuma zai ƙara taka rawa a zabuka
- Turaki ya ce PDP ta cika duk sharuddan doka, INEC ta sa ido kan tsaida ‘yan takara, kuma sulhu zai zo bayan kammala shari’o’i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi wata ganawa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a Abuja.
Jam'iyyar ta kai rikicin shugabancinta wajen tsohon shugaban ƙasar yayin da matsalar ke ƙara tsananta a jam’iyyar adawa.

Source: Twitter
PDP ta gana da Goodluck Jonathan a Abuja
Mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa, NWC, sun gana da Jonathan a ofishinsa da ke Maitama da ke Abuja, domin neman shawarwari da jagoranci, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
Ana hasashen zai tsaya takara, Jonathan ya saka labule da shugabannin PDP a Abuja
Ganawar ta samu halartar shugabannin jihohi na PDP, tsofaffin gwamnoni, mambobin BOT, da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan halin da PDP ke ciki, rikicin shugabanci, ƙoƙarin farfaɗo da jam’iyyar, da shirye-shiryen zaben gwamna.
Ziyarar ta zo ne yayin da ake samun ɓangarori biyu da ke ikirarin kujerar shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.
Abdulrahman Mohammed na samun goyon bayan ɓangaren da ke da alaƙa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, yayin da Turaki ke samun goyon bayan Bala Mohammed da Seyi Makinde.
Bayan taron, Turaki ya shaida wa manema labarai cewa sun je wajen Jonathan domin gabatar masa da sabon NWC da aka zaɓa.

Source: Facebook
Abin da PDP ta sanar da Jonathan
Turaki ya bayyana cewa sun sanar da Jonathan halin da PDP ke ciki, ƙalubale da kuma damar da jam’iyyar ke da ita nan gaba.
Ya ce Jonathan ya tabbatar har yanzu cikakken mamba ne mai kati na PDP, kuma yana ci gaba da kasancewa mai taka rawa a jam’iyyar.
“Ya tabbatar mana cewa zai ƙara taka rawa a harkokin PDP, musamman yayin da ake shirin zaɓukan Ekiti da babban zaɓen 2027,”
- In ji Turaki
Turaki ya ce maganganun Jonathan sun ƙarfafa gwiwar jam’iyyar, tare da ba su kwarin gwiwa kan makomar PDP a siyasance, cewar BusinessDay.
Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa PDP ita ce jam’iyyar da ta fi cancanta wajen yin takara da samun nasara a ƙasar nan.
Jam'iyyar PDP ta maka hukumar INEC a kotu
An ji cewa jam’iyyar PDP ta shigar da ƙara a gaban kotu tana neman a tilasta wa INEC saka sunan dan takararta a jerin ‘yan takarar zaben gwamnan Ekiti.
Jam’iyyar ta ce cire sunan Oluwole Oluyede barazana ce ga sahihancin zabe, tana zargin INEC da nuna son rai kan shugabancinta na ƙasa.
PDP ta jaddada cewa ta bi duk ka’idojin doka wajen yin zaben fitar da gwani a jihar, tana mai gargadin hukumar INEC da ta tsaya kan matsayinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
