Hadakar Atiku da Peter Obi Ta Kara Karfi, 'Dan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheka zuwa ADC

Hadakar Atiku da Peter Obi Ta Kara Karfi, 'Dan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheka zuwa ADC

  • 'Dan Majalisar wakilan tarayya, Hon. Murphy Osaro Omoruyi ya tattara kayansa ya bar jam'iyyar LP zuwa ADC a jihar Edo
  • Hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan jagoran LP kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya koma jam'iyyar ADC
  • Hon. Omoruyi ya ce duk da yadda ya nunawa LP halacci, amma lokaci ya yi zai bar ta saboda rigingimun cikin gida da suka dabaibaiye ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - Wani dan majalisar wakilai, Hon. Murphy Osaro Omoruyi, ya fice daga Jam’iyyar LP zuwa dandalin hadakar jam’iyyun adawa, wato ADC.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Hon. Omoruyi shi ne dan LP na karshe daga Jihar Edo a Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Jagororin ADC.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan ADC Hoto: @Atiku
Source: Facebook

'Dan Majalisar wakilai ya bar jam'iyyar LP

Hon. Omoruyi, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Egor/Ikpoba-Okha, ya ce ya bar LP ne bisa bukatar jama’arsa, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan barin kujerar minista, Badaru ya magantu kan jita jitar watsar da APC

Ya bayyana cewa tun bayan zabarsa a matsayin mamban Majalisar Tarayya, ya ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da muhimman ayyukan dokoki da sa ido kan ayyukan gwamnati a mazabarsa.

Da yake jawabi ga manema labarai a Birnin Benin, babban birnin Jihar Edo, Hon. Omoruyi ya ce yadda ya daure ya zauna a LP ya sa aka yi masa lakabi da “The Last Man Standing."

A cewarsa, wannan suna da aka lakaba masa ya nuna irin jajircewarsa da kuma biyayyar da ya yi wa jam'iyyar LP amma a yanzu ya zabi bin sawun jagoran jam'iyyar, Peter Obi.

Hon. Omoruyi ya fadi dalilin shiga ADC

A rahoton jaridar Guardian, 'dan Majalisar ya ce:

“Sai dai duk da kokarin da muka yi, rikice-rikicen da suka dabaibaye Jam’iyyar LP na ci gaba da faruwa kuma babu wata alamar magance su, hakan ya sa ba zai yiwu na ci gaba da zama ba."
“Na shiga tafiyar hadaka, ADC ne bayan na mika takardar murabus dina daga LP ga shugaban jam’iyya na mazabata da ke Karamar Hukumar Egor, a ranar 30 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya hango abin da zai wargaza jam'iyya, ya bada shawara tun wuri

“Bayan na shiga ADC a yau, na dauki alkawarin yin aiki kafada da kafada da shugabannin jam’iyyar, abokan hadaka da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta shugabanci nagari da wakilci mai inganci.
Hon. Omoruyi.
'Dan majalisar wakilai ta kasa daga jihar Edo, Hon. Murphy Osaro Omoruyi Hoto: Hon. Murphy Osaro Omoruyi
Source: Facebook

'Dan Majalisar ya kuma tabbatar wa al'ummar mazabarsa cewa yana tare da su kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya inganta rayuwarsu.

Ya kuma caccaki gwamnatin tarayya bisa yadda take kara kawo tsare-tsaren da ke kuntatawa 'yan Najeriya, inda ya ce babu hanyoyi da ababen more rayuwa sao dai tsadar rayuwa.

Atiku ya hakura da takara a 2027?

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya jaddada cewa ba gudu ba ja da baya a shirinsa na neman takara a xaben 2027.

Atiku ya yi zargin cewa wasu daga can gefe, na kokarin tsoma baki musamman wajen zabar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, gabanin zaben 2027.

Wazirin Adamawa ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun shafe kusan shekaru uku suna fuskantar matsin tattalin arziki da kuncin rayuwa karkashin mulkin Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262