Ana Hasashen Zai Tsaya Takara, Jonathan Ya Saka Labule da Shugabannin PDP a Abuja
- Shugaban PDP Tanimu Turaki ya jagoranci kwamitin ayyuka na kasa zuwa taron sirri da Goodluck Jonathan a ofishinsa na Maitama Abuja
- Wannan na daga cikin ƙoƙarin da Tanimu Turaki yake yi na sasanta rikicin cikin gida da ya daɗe yana dabaibaye PDP tun bayan zaɓen 2023
- Bayan kammala ganawar da aka fara da misalin karfe 6:00 na yamma, shugaban PDP ya fadi abubuwan da suka tattauna da Jonathan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A yau Talata, 6 ga watan Janairu, 2026, shugabannin jam’iyyar PDP na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Dr. Tanimu Turaki (SAN), sun gudanar da wata muhimmiyar ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
An fara ganawar, wadda aka gudanar a ofishin Jonathan da ke unguwar Maitama a birnin Abuja da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

Source: Twitter
Shugabannin PDP sun gana da Jonathan
Wannan taro na daga cikin ƙoƙarin da shugabannin jam’iyyar ke yi na sasanta rikicin cikin gida da ya daɗe yana dabaibaye jam’iyyar tun bayan zaɓen 2023, in ji rahoton Daily Trust.
Turaki, tare da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da wasu shugabannin jihohi, sun yi wa Jonathan bayani kan halin da jam’iyyar take ciki da kuma shari’o’in da ake yi a kotu.
Bayan taron, Turaki ya bayyana wa manema labarai cewa tsohon shugaban ƙasar ya jaddada goyon bayansa ga jam'iyyar.
A cewar Turaki, Jonathan ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta yi masa komai a rayuwa, don haka zai yi iya ƙoƙarinsa don ganin ya taimaka mata ta fita daga mawuyacin halin da take ciki.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafin PDP na X ta ruwaito Jonathan yana cewa:
"Na ci gajiyar wannan jam'iyya, domin ita ta ba ni damar zama mataimakin gwamna, da gwamna, da mataimakin shugaban kasa da kuma shugaban kasa."
Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP
A halin yanzu, jam’iyyar PDP ta kasu gida biyu; ɓangaren Dr. Tanimu Turaki wanda gwamnonin Bauchi da Oyo ke marawa baya, da kuma ɓangaren Abdulrahman Muhammed wanda tsagin Minista Nyesom Wike ke goyon baya.
Wannan rarrabuwar kai ta sanya hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) shiga tsakani, kamar yadda rahoton jaridar Channels TV ya nuna.
A ranar 19 ga Disamba, 2025, muka ruwaito cewa shugaban INEC, Joash Amupitan, ya gana da ɓangarorin biyu domin warware rikicin takardun da hukumar ke samu masu karo da juna.

Source: Twitter
Rikicin PDP da batun zabukan 2026
Shigar INEC tsakani ya zama dole ne domin tunkarar zaɓukan kananan hukumomin Abuja da kuma zaɓukan gwamnonin jihohin Osun da Ekiti da za a gudanar a tsakiyar shekarar 2026.
Masana dai sun nuna damuwarsu kan yadda rikicin zai iya shafar sahihancin zaɓukan tare da ba kowanne bangare shawarar yin abin da ya dace don ci gaban jam'iyyar.
Ana kallon ganawar Jonathan da kwamitin Turaki a matsayin wani babban mataki na neman gyara siyasa da kuma haɗa kan dukkan jiga-jigan jam’iyyar kafin waɗannan muhimman zaɓuka.
'Ana shirin dawo da Jonathan' - Bashir Ahmad
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad ya ce akwai wani shiri da ake kullawa kan Goodluck Ebele Jonathan.
Bashir Ahmad ya bayyana cewa akwai masu son ganin an kawo tsohon shugaban kasa ya sake neman takara a zaben shekarar 2027.
'Dan siyasar ya bayyana cewa ana son yin wannan shirin ne don samun kuri'un 'yan Arewa, yankin da ya fi ko ina yawan al'umma a kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


