Hadimin Tinubu Ya Hango Abin da Zai Faru da Peter Obi a Jam'iyyar ADC

Hadimin Tinubu Ya Hango Abin da Zai Faru da Peter Obi a Jam'iyyar ADC

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya sauya sheka daga jam'iyyar LP zuwa ADC a makon da ya wuce
  • Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Peter Obi ba zai samu abin da yake so ba a ADC
  • Bwala ya kuma bayyana cewa idan Peter Obi ya tsaya takara a zaben 2027, ba zai samu ko rabin kuri'un da ya samu ba a 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Daniel Bwala, mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara na musamman kan yada manufofi, ya yi magana kan Peter Obi.

Daniel Bwala ya ce Peter Obi ba zai zama ɗan takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ADC ba.

Bwala ya ragargaji Peter Obi
Daniel Bwala da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi Hoto: @BwalaDaniel, @PeterObi
Source: Twitter

Daniel Bwala ya faɗi hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin The Clarity Zone Podcast.

Kara karanta wannan

Rigima ta kara zafi, sakataren APC na kasa ya nemi Ministan Tinubu ya yi murabus

Me hadimin Tinubu ya ce kan Peter Obi?

Hadimin shugaban kasan ya yi ikirarin cewa Peter Obi ba shi da karfin jagoranci da zai ba shi damar zama jagora na kowace haɗakar jam’iyyun siyasa.

Mai ba shugaban kasar shawara ya kara da cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra zai kare da tsayawa takarar zaɓe na gaba ne a wata jam’iyya daban ba ADC ba.

A cewarsa, Peter Obi ya rasa ikon tsarin siyasar da ya gina bayan zaɓen 2023, ciki har da tasirinsa a majalisar tarayya.

“Bayan zaɓe, ya rasa duk mutanen da yake jagoranta. Yana da ’yan majalisar wakilai a baya, yanzu nawa ne suke cikin majalisar tarayya?”
“Gwamnan da yake da shi kaɗai, yana tare da shi ne ko yana tare da mu? A gaskiya ban ga alamar da ke nuna yana tare da shi a halin yanzu ba. Duk zaɓubbukan da ya zagaya Najeriya yana tallata ’yan takara, duk sun faɗi.”

- Daniel Bwala

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Wike ya hango abin da zai zama karshensa a siyasa

Bwala ya soki magoya bayan Peter Obi

Daniel Bwala ya kuma soki magoya bayan Peter Obi a kafafen sada zumunta, yana mai cewa:

“Sojojin da yake da su a kafafen sada zumunta suna cin zarafin mutane. Suna cewa kana da fuska biyu, kana canza jam’iyya. Haka suke yi kullum.”
“Amma idan ka ce ubangidansu shi ma yana ta canza jam’iyya kamar ɗan wasan Premier League da ke canza kulob duk kakar wasa, ba sa son jin haka.”
Daniel Bwala ya ragargaji magoya bayan Peter Obi
Hadimin shugaban kasar Najeriya, Daniel Bwala Hoto: @BwalaDaniel
Source: UGC

An soki Peter Obi kan sauya sheka

Mai bai shugaban kasar shawara ya kuma zargi Peter Obi da munafunci game da batun biyayya ga jam’iyya, yana mai cewa tsohon gwamnan ya sha sauya jam’iyyun siyasa.

“Ya fara ne da PDP, daga nan ya koma APGA. Daga APGA ya sake dawowa PDP. Daga PDP kuma ya koma LP.”
“Ba zai zama ɗan takarar shugaban kasa ba, kuma ba zai zama mataimakin ɗan takara ba. Peter Obi zai tsaya takara ne a wata jam’iyya daban ba LP ba, kuma ba ADC ba.”

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya sha alwashin korar gwamna daga mulki, zai iya yin komai a 2027

- Daniel Bwala

Daniel Bwala ya kara da cewa Peter Obi ba zai samu ko kashi ɗaya cikin huɗu na kuri’un da ya samu a zaɓen shugaban kasa na 2023 ba.

Atiku ya yi wa Peter Obi maraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi wa Peter Obi, maraba zuwa jam'iyyar ADC.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana sauya shekar Peter Obi zuwa ADC a matsayin babban ci gaba a tarihin kawancen siyasa a Najeriya.

Atiku Abubakar ya bayyana fatan cewa shigowar Peter Obi jam’iyyar za ta kara dankon hadin kai a tsakanin ’yan adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng