PDP Ta kai INEC Kotu kan Cire Sunan Dan Takararta a Zaben Gwamnan Ekiti

PDP Ta kai INEC Kotu kan Cire Sunan Dan Takararta a Zaben Gwamnan Ekiti

  • Jam’iyyar PDP ta shigar da ƙara a gaban kotu tana neman a tilasta wa INEC saka sunan dan takararta a jerin ‘yan takarar zaben gwamnan Ekiti
  • Jam’iyyar ta ce cire sunan Oluwole Oluyede barazana ce ga sahihancin zabe, tana zargin INEC da nuna son rai kan shugabancinta na ƙasa
  • PDP ta jaddada cewa ta bi duk ka’idojin doka wajen yin zaben fitar da gwani a jihar, tana mai gargadin hukumar INEC da ta tsaya kan matsayinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ekiti – Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ta fara daukar matakin shari’a a kan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), domin tilasta mata saka sunan dan takararta, Oluwole Oluyede, a jerin ‘yan takarar zaben gwamnan jihar Ekiti.

Jam’iyyar ta ce matakin da INEC ta dauka na cire sunan dan takarar nata barazana ce ga sahihancin zabe, musamman ganin cewa an riga an sanya ranar gudanar da zaben a 20, Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damƙe ƴan ƙunar baƙin wake 2 kan tashin bam a masallacin Maiduguri

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa.
Shugaban PDP, Tanimu Turaki da shugaban INEC. Hoto: PDP Official
Source: Facebook

Sakataren yada labarai na kasa na PDP, Ini Ememobong, ne ya bayyana hakan a sanarwar da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X.

Zargin PDP kan hukumar INEC

Ememobong ya bayyana cewa PDP na ganin matakin INEC a matsayin wata shaida ta nuna son rai da nuna bambanci kan kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar karkashin jagorancin Taminu Turaki.

A cewarsa, cire sunan Oluyede daga jerin ‘yan takarar zaben gwamnan Ekiti wata babbar barazana ce ga ‘yanci da amincin tsarin zabe a Najeriya.

Ya ce:

“Cire sunan dan takararmu da cikakkun bayanansa daga jerin ‘yan takarar zaben gwamna na Ekiti a 2026 kara tabbatarwa ce ta irin son ran da shugabancin INEC na yanzu ke nunawa kan harkokin jam’iyyar PDP.”

PDP ta zabi dan takarar gwamna a Ekiti

PDP ta bayyana cewa Oluyede ya samu nasara ne a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar daga 8 zuwa safiyar 9, Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

PDP na tsaka mai wuya da INEC ta fitar da sunayen 'yan takarar gwamna a zaben Ekiti

Punch ta wallafa cewa jam’iyyar ta ce INEC ta samu cikakken labari kan zaben fidda gwanin, ta kuma halarta tare da sanya idanu kan yadda aka gudanar da shi.

Ememobong ya kara da cewa INEC ta fitar da rahotannin da ke tabbatar da cewa an gudanar da zaben fidda gwanin bisa tanadin doka, sannan ta bayar da damar shigar da bayanan dan takara a shafin yanar gizo na hukumar.

Oluwole Oluyede na PDP
Dan takatar PDP a zaben Ekiti, Oluwole Oluyede. Hoto: PDP Official
Source: Facebook

Sai dai ya zargi INEC da cewa daga bisani ta toshe wannan dama kwanaki kadan kafin wa’adin karshe na mika takardun dan takara, lamarin da ya tilasta PDP mika takardun ta hannu a ofishin INEC, inda aka karba tare da tabbatar da karbarsu.

'Yan majalisar PDP sun koma APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan majalisar wakilai karkashin jam'iyyar PDP daga jihar Rivers sun koma APC mai mulki a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan gwamna Siminalayi Fubara ya sanar da komawa APC tare da cewa zai marawa Bola Tinubu baya a 2027.

Sauya shekar ya kara sanya APC kara karfi jihar Rivers duk da sabanin da ake samu tsakanin gwamna Fubara da minista Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng