Sauya Sheka: 'Yan APC Sun Tattauna da Abba ba Tare da Kwankwaso ba
- Ana ci gaba da samun ruɗani a Kano kan shirin da ake cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai fice daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya girgiza Kwankwasiyya
- 'Dan majalisa tarayya, Kabiru Alhassan Rurum ya tabbatar da cewa sun tattauna da Abba Kabir Yusuf game da sauya sheka ba tare da Rabiu Musa Kwankwaso ba
- Wani masanin siyasa ya yi gargaɗin cewa matakin zai sauya lissafin siyasa a Kano, tare da raunana NNPP da kawo sababbin ƙalubale kafin zaben 2027 a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rikici da ruɗani na ci gaba da ƙara ƙamari a siyasar Kano sakamakon shirin da ake cewa gwamna Abba Kabir Yusuf yana yi na ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, matakin da zai iya raba shi da jagoransa na siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso.
Wannan lamari ya haifar da jita-jita da tattaunawa a tsakanin mambobin Kwankwasiyya, inda ake ganin ficewar gwamnan za ta iya kawo babbar baraka a siyasar da Kwankwaso ya assasa a jihar.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Abba Kabir Yusuf ya yi wata ganawa da 'yan APC a shirin sauya sheka da ya ke son yi daga NNPP zuwa APC.
Tattaunawar Gwamna Abba da 'yan APC
Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Rt Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya tabbatar da cewa ya gana da Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan shirin ficewar gwamnan daga NNPP.
Rurum, wanda yanzu ke wakiltar mazabar Rano/Bunkure/Kibiya a majalisar wakilai bayan ficewarsa daga NNPP zuwa APC, ya bayyana cewa ba a tattauna batun Kwankwaso a ganawar ba.
Aminiya ta wallafa a Facebook cewa ya ce duk tattaunawar da suka yi ta shafi dabarun siyasa ne da ke kewaye da shirin ficewar gwamnan, ba tare da shiga batun Kwankwasiyya ko jagorancinsa ba.
Kwankwaso ya gana da 'yan majalisar Kano
Rahotanni sun ce Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wata ganawar a ɓoye da shugaban majalisar dokokin Kano, a wani yunƙuri na ƙarshe domin dakatar da ficewar gwamnan.
A lokaci guda kuma, ’yan majalisar jihar da ke biyayya ga Abba Kabir Yusuf an shirya za su gana da gwamnan domin bayyana goyon bayansu a hukumance.

Source: Facebook
Wata majiya kusa da Kwankwaso ta ce tsohon gwamnan ya shiga matuƙar takaici, inda ya fara kasa yarda cewa Abba Kabir Yusuf zai iya ƙalubalantar sa a fili.
Nazarin masana kan tasirin siyasa
Masani kan harkokin siyasa a Kano, Dr Kabiru Sa’idu Sufi, ya ce idan Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP, hakan zai sauya lissafin siyasa sosai a jihar.
Ya yi nuni da cewa duk da cewa gwamna na da ƙarfin kujerarsa, matakin zai haifar da rashin jin daɗi da rarrabuwar kawuna, tare da raunana NNPP da raba Kwankwasiyya gida biyu.
Sufi ya ƙara da cewa APC na fatan kara samun gwamnoni gabanin 2027, amma ya jaddada cewa kasancewa a kan mulki kaɗai ba ya tabbatar da nasara a zaɓe.
Ciyama na Tsanyawa ya je gidan Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa shugaban karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano, Hon. Abdullahi Ishaq ya ziyarci Sanata Rabiu Kwankwaso.
Shugaban karamar hukumar ya ziyarci jagoran ne a daidai lokacin da 'yan uwansa ciyamomi ke kira da a shiga jam'iyyar APC mai mulki.
Shugabannin kananan hukumomi kimamin 30 ne suka yi kira ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf da su ja su zuwa APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


