Shiga APC: Ciyaman Ya Rabu da 'Yunkurin' Abba a Kano, Ya Tafi Gidan Kwankwaso

Shiga APC: Ciyaman Ya Rabu da 'Yunkurin' Abba a Kano, Ya Tafi Gidan Kwankwaso

  • Ana ci gaba da rade-radin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin barin NNPP zuwa APC tare da goyon bayan shugabanni da dama
  • Wasu shugabannin kananan hukumomi sun nuna shirin bin gwamnan zuwa APC, yayin da wasu suka jaddada biyayyarsu ga Kwankwasiyya
  • Ziyarar shugaban karamar hukumar Tsanyawa zuwa ga jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ta sake fito da rarrabuwar kai a siyasar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – A daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, al’amuran siyasa sun ɗauki sabon salo a jihar.

Rahotanni na nuni da cewa gwamnan ba zai yi wannan sauyi shi kaɗai ba, domin ana zargin yana shirin tafiya tare da akalla shugabannin kananan hukumomi 35 daga cikin 44.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Shugaban karamar hukuma ya rasu a Yobe bayan doguwar jinya

Tawagar Tsanyawa da ta gana da Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso tare da tawagar ciyaman Tsanyawa. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Ciyaman Tsanyawa ya ziyarci Kwankwaso

A cikin wannan yanayi, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook cewa shugaban karamar hukumar Tsanyawa, Hon. Abdullahi Ishaq, ya kai ziyara ta girmamawa ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Majiyoyi sun ce ziyarar da Hon Abdullahi Ishaq ya kai wa Kwankwaso na nufin tabbatar da matsayinsa na ci gaba da zama a jam’iyyar NNPP, a daidai lokacin da ake zargin wasu shugabannin kananan hukumomi na shirin komawa APC.

Masu sharhi kan siyasa a Kano na ganin cewa wannan ziyara ta sake fayyace cewa ba duka shugabannin kananan hukumomi ke goyon bayan shirin gwamnan na sauya sheƙa ba

Jerin ciyamomin da suka goyi bayan Abba

Bisa bayanan da shafin Arewa Update ya wallafa a Facebook, an ce akwai kananan hukumomi 31 da aka ruwaito cewa shugabanninsu sun nuna niyyar bin Abba Kabir Yusuf zuwa APC.

Wadannan kananan hukumomi sun hada da:

Kara karanta wannan

Yadda Abba ya lashi takobin shiga APC ko zai wargaje da Kwankwaso

Ajingi, Albasu, Bagwai, Bichi, Bunkure, Dala, Danbatta, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Doguwa, Gabasawa, Garko, Gaya, Gezawa, Ghari, Gwale, Gwarzo, Kabo, KMC, Kiru, Makoda, Nassarawa, Rano, Rimin Gado, Rogo, Tarauni, Tofa, Tudun Wada, Ungogo, Warawa da Wudil.

Ciyamomin da suka tsaya da Kwankwaso

A bangaren wadanda suka bayyana biyayyarsu ga Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP, rahotanni sun nuna cewa shugabannin kananan hukumomi biyu ne kawai suka fito fili.

Abba Kabir Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso
Abba Kabir na zaune tare da Rabiu Kwankwaso a wani taro. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Su ne kananan hukumomin Kura da Tsanyawa, inda aka ce sun jaddada cewa za su ci gaba da zama a NNPP tare da Rabiu Musa Kwankwaso.

Ciyamomin da ba su yi matsaya ba

Sai dai duk da wannan rabuwar kai, akwai wasu kananan hukumomi 11 da ba a samu cikakken bayani kan matsayinsu ba.

Wadannan kananan hukumomi su ne Bebeji, Fagge, Garun Mallam, Karaye, Kibiya, Kumbotso, Madobi, Minjibir, Shanono, Sumaila da Takai.

Masana siyasa na ganin cewa idan har rade-radin ficewar Abba Kabir Yusuf ya tabbata, hakan na iya haifar da gagarumin sauyin siyasa a Kano gabanin babban zaben 2027.

Wata majiya ta ce Abba zai shiga APC

A wani labarin siyasar Kano, mun kawo muku cewa wata majiya daga fadar gwamnatin jihar ta ce Abba Kabir Yusuf ya shirya shiga APC.

Kara karanta wannan

'Mun amince Abba da Kwankwaso su jagorance mu zuwa APC,' in ji ciyamomin Kano

Majiyar ta bayyana cewa gwamnan zai koma APC ba makawa ko da za a samu sabanin siyasa tsakaninsa da Rabiu Musa Kwankwaso.

An bayyana cewa sauya shekar na da alaka da rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar NNPP da ake ganin zai shafi zaben 2027 a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng