Yadda Abba Ya Lashi Takobin Shiga APC ko zai Wargaza Alaka da Kwankwaso

Yadda Abba Ya Lashi Takobin Shiga APC ko zai Wargaza Alaka da Kwankwaso

  • Rade-radin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheka daga NNPP zuwa APC ya jefa tafiyar Kwankwasiyya cikin ruɗani
  • Wasu majiyoyi sun ce gwamnan ba zai sauya matsaya ba, ko da hakan zai haifar da rabuwar kai tsakaninsa da Rabiu Musa Kwankwaso
  • Rahotanni sun nuna cewa ana danganta wannan yunƙuri na shiga APC da rikice-rikicen cikin gida a NNPP da kuma lissafin siyasar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Tattaunawa da rade-radi sun ƙara ƙamari a siyasar Kano bayan bayyanar labarai da ke nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na dab da sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.

Wannan lamari ya fara haifar da rabuwar kai a tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

'Mun amince Abba da Kwankwaso su jagorance mu zuwa APC,' in ji ciyamomin Kano

Abba Kabir Yusuf, Rabiu Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa majiyoyi da dama sun ce wannan shiri ya haifar da rikicewar fahimta tsakanin manyan jiga-jigan Kwankwasiyya, musamman ganin rawar da Kwankwaso ya taka wajen nasarar Abba Kabir Yusuf.

Sauya shekar da ake hasashe na zuwa ne a lokacin da siyasar Kano ke fuskantar sababbin tsare-tsare, inda ake ganin matakin na iya sake buɗe tsofaffin rikice-rikice tare da sauya yanayin shirin jam’iyyu gabanin babban zaben 2027.

Abba Kabir zai tsaya kan matsayarsa

Wasu majiyoyi sun shaida cewa gwamnan ya riga ya yanke shawara kan sauya shekar, inda suka ce ba ja da baya ko da hakan zai kai ga rabuwa tsakaninsa da Kwankwaso, wanda shi ne ya kafa tafiyar Kwankwasiyya.

A cewar majiyoyin, wannan yunƙuri ya sake tayar da tsofaffin hamayya a siyasar Kano, tare da jefa tambayoyi kan makomar Kwankwasiyya da kuma yadda za a shiga zaben 2027.

Sun ƙara da cewa gwamnan ya kai wannan matsaya ne bayan shawarwari masu zurfi da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da ’yan majalisar dokokin jihar Kano, shugabannin ƙananan hukumomi da kuma ’yan majalisar tarayya daga jihar.

Kara karanta wannan

Rabuwar Abba da Kwankwaso: Sanata Hanga ya gargadi 'maciya amana' a Kwankwasiyya

Batun hana Abba takara a 2027

Wani babban mai taimaka wa gwamnan, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce babban dalilin wannan shawara shi ne rikice-rikicen cikin gida da ke addabar NNPP, lamarin da zai iya kawo cikas ga burin Abba Kabir Yusuf na neman wa’adi na biyu.

Majiyar ta ce ana ganin NNPP ba ta da ƙarfi a halin yanzu saboda tana gaban kotu, inda ya yi zargin cewa ko da gwamnan ya ci gaba da zama a jam’iyyar, ba za a ba shi tikitin takara ba.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa akwai fargaba a cikin da’irar Kwankwaso cewa ayyukan da Abba Kabir Yusuf ke yi a fili a jihar na iya rufe tarihin Kwankwaso, wanda hakan ke sa wasu ba sa son gwamnan ya ci gaba da mulki.

Sanata Hanga na tare da Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rufa'i Hanga na jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa maciya amana ne ke kokarin raba Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Majiyoyi sun fadi ranar da Gwamnan Kano, Abba zai sanar da komawa APC

A wata hira da ya yi da manema labarai, Sanatan ya ce zai tsaya tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso idan Abba ya juya masa baya.

A karshe, Sanata Hanga ya yi kira ga Abba Kabir Yusuf da ya zauna a NNPP, domin a cewarsa, bai ga wani abu da zai samu a APC ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng