'Mun Amince Abba da Kwankwaso Su Jagorance Mu zuwa APC,' In Ji Ciyamomin Kano
- Wasu ciyamomi a Kano sun yi kira ga Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf da su jagorance su zuwa jam'iyyar APC
- Masu ruwa da tsaki na NNPP sun bayyana cewa komawa APC za ta tabbatar da dorewar zaman lafiya da ci gaban ayyukan raya kasa a jihar
- Bashir Ahmad ya bayyana yakinin cewa sauya shekar Gwamna Abba Yusuf zuwa jam'iyyar APC za ta tabbata nan da kwanaki masu zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Kungiyoyi, shugabannin kananan hukumomi da kusoshin jam'iyyar NNPP sun fara kiran Gwamna Abba Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso su koma APC.
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, Bashir Ahmed, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, ya ce yana da tabbacin Abba zai bar NNPP zuwa APC a kwanaki masu zuwa.

Source: Twitter
Sakon karamar hukumar Bichi ga Abba
Jim kadan bayan hakan, Aliyu Isa Aliyu, kwamishinan ma'aikatar ci gaban tsuntsaye da dabbobi ta Kano, ya fitar da wani bidiyo a shafinsa na Facebook.
A cikin bidiyon, an ji mataimakin shugaban karamar hukumar Bichi, Abubakar Sule Babangida ya na magana a madadin shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata.
Abubakar Sule ya ce:
"A yau Litinin, 29 ga watan Disamba, 2025, mun zauna da masu ruwa da tsaki, wadanda suka hada da zababbun shugabanni na karamar hukumar Bichi, da nadaddu, da masu ba da shawara, da jami'ai 30, da Kwakwasiyya Lafiya Jari, da Kano CRC, da masu mukaman gwamnatin jiha, da kusoshi, mun cimma matsaya.
"Mun cimma matsaya a kan muna kira ga jagora, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da mai girma gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da su ja mu, su kai mu jam'iyyar APC domin ci gaba da ayyukan raya kasa da al'ummar Bichi da kasa ba ki daya."
Ciyaman na Albasu na so a shiga APC
A karamar hukumar Albasun jihar Kano, nan ma dai ba ta canja zani ba, inda masu ruwa da tsaki na jam'iyyar NNPP suka yi taro, tare da yanke shawarar yin kira ga Abba da Kwankwaso su shiga APC.
Masu ruwa da tsakin, a cikin wani bidiyo da Abdulhamid Yusuf Uba ya wallafa a shafinsa na Facebook, sun ce akwai bukatar Abba da Kwankwaso su hada kansu su jagoranci 'yan Kwankwasiyya zuwa APC a Kano.
Wanda ya yi magana a madadin jagororin, ya ce:
"Wannan shawara ta biyo bayan irin hangen nesa da masu da tsaki suka yi na cewa yin hakan shi ne zai taimaka wajen dorewar zaman lafiya da ci gaban al'ummarmu na jihar Kano da karfafa gwiwa ga Abba ya ci gaba da ayyukan alheri da yake yi a Kano.
"Muna ganin cewa, la'akari da yadda siyasar kasar nan take tafiya, idan aka koma jam'iyyar APC, za a samu dawwamammen zaman lafiya, da dorewar aikace-aikace da mai girma gwamna yake yi a fadin jihar Kano."

Source: Facebook
Danbatta ta bi sahun masu son koma wa APC
A bangaren karamar hukumar Danbatta, shugaban karamar hukumar, Hon. Jamilu Abubakar Danbatta ya yi bukaci jagoran NNPP Rabiʼu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Yusuf su ja ragamarsu zuwa APC.
Hon. Jamilu Danbatta ya ce:
"A madadin karamar hukumar Danbatta, da jagororinmu da kwamishinoni, da dukkan majalisa da al'umar Danmbatta, muna rokon Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Yusuf, su hada kai, su dauke mu su kai mu jam'iyyar APC."
Mahalarta wannan taro sun nuna amincewarsu ga wannan magana da shugaban karamar hukumar ya yi, tare da nuna goyon bayansu na shiga jam'iyyar APC.
Wike ya aika sako ga masu shiga APC
A wani labari, mun ruwaito cewa, Nyesom Wike, ya gargaɗi ‘yan siyasa cewa shiga APC ko nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu ba ya nufin tabbacin samun tikitin wa’adi na biyu kai tsaye.
Wike ya yi wannan gargaɗin ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a ƙaramar hukumar Emohua da ke Rivers, a wani bangare na ziyarce-ziyarcensa na tuntubar jama'a a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa siyasa dole ta kasance bisa yarjejeniya, tare da cika alƙawura, yana mai cewa biyayya ba tare da tsari ko cika alƙawari ba, ba ta da wani alfanu ga jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


