Sanata Ya Hango Abin da Zai Wargaza APC duk da Yawan Sauya Shekar 'Yan Adawa

Sanata Ya Hango Abin da Zai Wargaza APC duk da Yawan Sauya Shekar 'Yan Adawa

  • 'Yan jam'iyyun adawa musamman PDP na ci gaba da tururuwar sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Sanata Abba Moro na Kudancin Benuwai ya nuna damuwa kan yadda mambobin PDP ke ci gaba da barin jam'iyyar zuwa APC
  • Sai dai, shugaban masu rinjayen na majalisar dattawa ya bayyana illar da hakan yake da ita ga APC da dimokuradiyyar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Abba Moro, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, ya ce jam’iyyar APC ta zama kamar jirgi da aka cika fiye da kima a tsakiyar ruwa.

Sanata Abba Moro ya kara da cewa yawaitar sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki na haifar da babbar barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

Sanata Abba Moro ya koka kan yawan komawa APC
Sanata Abba Moro a zauren majalisar dattawa Hoto: Comrade Abba Moro
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce Sanata Abba Moro ya faɗi hakan ne yayin zaman majalisar dattawa na ranar Talata, 23 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Bayan ƴan majalisar wakilai 6, sanatoci 2 masu biyayya ga Wike sun fice daga PDP

Sanatoci sun koma APC daga jam'iyyar PDP

Sanatan ya yi magana ne bayan sanatoci biyu: Barinada Mpigi da Allwell Onyesoh, masu wakiltar Rivers ta Kudu-maso-Gabas da Rivers ta Gabas, sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Shugabanni da ’yan jam’iyyar APC sun halarci sauya sheƙar, inda aka shigar da su cikin zauren Majalisar bayan Majalisar ta dakatar da dokokinta na wucin gadi.

Me Sanatan ya ce kan yawan shiga APC?

Da yake martani bayan an dawo zama, Sanata Moro ya bayyana lamarin a matsayin kaucewa daga kan dimokuradiyya, yana mai cewa irin hakan na raunana adawa da daidaiton dimokuaɗiyya.

Ya nanata cewa sauya shekar ba alheri ba ne ga dimokuradiyyar.Najeriya, jaridar The Sun ta dauko labarin.

"Dangane da abin da ya faru yanzu, ina so na ce abokan aikina a wannan bangaren na adawa sun yi amfani da ’yancinsu na yin tarayya da duk inda suka ga dama.”
“Amma bari na faɗa a nan, kamar yadda na taɓa faɗa a baya, idan ka cika jirgi a tsakiyar ruwa, abin da zai iya faruwa shi ne jirgin ya kife.”

Kara karanta wannan

'Yan majalisar tarayya 6 sun gaji da zama a PDP, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

“Mai girma shugaban majalisa, ina ganin idan mutane za su tafi, ya kamata su tafi da cikakkiyar gamsuwa, ba wai su ba da hoton cewa PDP ko adawa gaba ɗaya na dab da rushewa ba.”
“Kun sani, a al’adarmu, ba za ka bugi yaro ka ce masa kada ya yi kuka ba.”
“Na ga abin ya ɗan baƙanta mini rai ganin cewa shugaban majalisa na taya kansa da jam’iyyarsa murna kan wannan hatsarin karkatar da dimokuraɗiyyar Najeriya.”
“Ina so na nanata cewa wannan ba alheri ba ne ga dimokiraɗiyya.”

- Sanata Abba Moro

Sanata Abba Moro ya nuna damuwa kan dimokuradiyyar Najeriya
Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro Hoto: Comrade Abba Moro
Source: Twitter

Shugaban majalisa ya yi katsalandan

A daidai wannan gabar, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi katsalandan inda ya bukaci Moro da ya taƙaita kansa kan batun da ke gaban Majalisa.

Sai Sanata Moro ya kara da cewa:

"Akasin abin da ake kokarin nuna wa mutane, ina so na nanata cewa wannan bangaren na adawa ba ya rushewa.”
“Za mu ci gaba da aiki domin muradun Najeriya daga wannan ɓangaren.”

'Yan majalisa sun fice daga PDP zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar PDP daga jihar Rivers sun sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Biki wan shagali: APC ta shirya gagarumar tarba ga Gwamna Mutfwang

'Yan majalisar wakilan da suka sauya sheka sun hada da Dumnamere Dekor, Solomon Bob, Hart Cyril, Victor Obuzor, Blessing Amadi, da Felix Nweke.

Sauya shekar ta sanya jam'iyyar PDP ta koma tana da 'yan majalisar wakilai guda uku kacal da suka fito daga jihar Rivers.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng