2027: Kawu Sumaila Ya Fadi Zabinsa daga cikin Masu Son Takarar Gwamna a Kano
- Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya ce ba shi da niyyar tsayawa takarar gwamnan Kano a 2027
- Ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci a wajensa shi ne ci gaba da bunkasar jiharsa ta Kano yadda ya kamata
- Sanatan ya yi tsokaci kan jita-jitar sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC, da kuma alakar Ganduje da Kwankwaso
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sanata Kawu Sumaila ya bayyana matsayarsa kan siyasar Kano gabanin babban zaɓen 2027, inda ya ce ba shi da wani buri ta tsayawa takarar gwamnan jihar.
Sanatan, wanda ya taba zama ƙusa a jam’iyyar NNPP kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa APC ya ce ci gaban Kano ne burinsa.

Source: Facebook
Sanata Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Lumana Radio, wadda aka wallafa a shafin Facebook.
Kawu Sumaila ya magantu kan siyasar Kano
A cewarsa, duk da hayaniyar siyasa da ake ta yi, abin da ya fi muhimmanci a wajensa shi ne a samu shugabanci nagari da zai hada kan al’ummar Kano, tare da kai jihar matakin ci gaba da ake bukata.
A yayin hirar, Sanata Kawu Sumaila ya jaddada cewa ba zai mara wa kowa baya ba illa mai hangen nesa da jajircewa wajen ciyar da Kano gaba.
A kalamansa, ya ce:
“Ba ingantacce kake so ba wanda zai taimaki Kano? Ya hada kan Kano ta ci gaba? Ni ma shi nake nema.”
Sanatan ya bayyana cewa wannan ne ainihin burinsa, kuma hakan ne zai jagoranci duk wani matsayi da zai dauka a siyasa.
Dangane da jita-jitar cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin sauya sheka zuwa APC, Kawu Sumaila ya nuna cewa bai ga matsala a ciki ba.
Ya ce:
“Allah Ya kawo shi lafiya, ya sa ya zama alheri a Kano.”
Ra’ayin Kawu Sumaila kan Ganduje da Kwankwaso
Da aka tambaye shi kan yiwuwar dawowar tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso APC, da kuma ko hakan ba zai haifar da matsala tsakanin sa da Abdullahi Umar Ganduje ba, Kawu Sumaila ya ce mafita ita ce tattaunawa.
Ya jaddada cewa manyan ‘yan siyasa ya kamata su zauna su fahimci juna domin amfanin Kano da Najeriya gaba ɗaya, kuma su kaɗai ne za su iya kawo ƙarshen matsalar da ke tsakaninsu.

Source: Twitter
Kan batun idan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ba wa daya daga cikin su fifiko, Sanatan ya ce hakan ya danganta da yadda Shugaban Ƙasar yake son a tafiyar da aiki, da kuma abin da ya ji daga bangarorin biyu.
A cewarsa:
“Ganduje ya fi sanin Kwankwaso, Kwankwaso ya fi sanin Ganduje.”
Kawu Sumaila ya ce rashin zama a tattauna tsakanin manyan ‘yan siyasan biyu ne ya jawo rashin fahimtar juna, yana mai nuni da cewa tattaunawa da yafiya su ne mabuɗin warware sabanin siyasa a Kano.
NNPP ta soki masu barin jam'iyya
A baya, mun wallafa cewa Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ajuji Ahmed, ya yi watsi da ‘ya’yan jam’iyyar da suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu a sassan Najeriya.
Ahmed ya ce jam’iyyar ba ta yi asara da ficewarsu ba. A cewarsa, waɗanda suka bar NNPP sun ɗauki hanyar da za ta cika da rudani da ƙalubale a tafiyar siyasarsu.
Ajuji Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Disamba, 2025, yayin taron karo na goma na kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP a Abuja.
Asali: Legit.ng


