Abin da Abba Ya Shaida wa Zababbun Shugabannin Jam'iyyar NNPP

Abin da Abba Ya Shaida wa Zababbun Shugabannin Jam'iyyar NNPP

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci shugabannin NNPP da aka zaba su kasance masu jajircewa da haɗin kai don ci gabansu
  • Gwamnan ya ba su wannan karfin gwiwa ne jim kadan bayan an rantsar da sababbin Shugabannin NNPP a babban birnin tarayya
  • Jagoran jam'iyyar na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kuma zaburar da Shugabannin gabanin babban zaɓe da ke tafe

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga shugabannin ƙasa na Jam’iyyar NNPP da aka zaɓa da su kasance masu jajircewa, aiki tukuru, da haɗin.

Ya bayyana cewa idan suka yi haka, zai taimaka matuka wajen ƙarfafa jam’iyyar domin cimma manufofinta na siyasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnoni na shiga APC, Kwankwaso ya yi magana kan Abba Kabir da NNPP

Kwankwaso da Abba sun mika sakonni Ga shugabannin NNPP
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Wannan jawabi ya fito ne a cikin sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya hannu a ranar Asabar, kuma ya wallafa a shafin Facebook.

Abba ya yi kira ga shugabannin NNPP

Gwamna Abba ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi ga wakilan taro a bikin rantsar da sababbin shugabannin ƙasa na NNPP da aka yi a Abuja.

Ya kuma sake tabbatar da jajircewar jam’iyyar wajen kyakkyawan shugabanci, kula da jin dadin al’umma, da kare ka’idojin dimokuradiyya a duk fadin Najeriya.

Ya bukaci ƴan jam’iyya a duk matakai da su rungumi hadin kai, biyayya, da sadaukarwa a matsayin muhimman kayan aiki na cimma burin al’ummar Najeriya baki ɗaya.

Kwankwaso ya zaburar da ƴan jam'iyyar NNPP

A nasa jawabi, jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya umarci shugabannin ƙasa da aka sake zaɓa da su ƙara himma .

Ya nemi su yi ƙoƙari wajen jagorantar jam’iyyar zuwa manyan nasarori a zabuka fiye da abin da aka samu a baya.

Kara karanta wannan

Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC

Daruruwan ƴan NNPPA sun halarci taron jam'iyya a Abuja
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Ajuji Ahmed Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Taron rantsarwa ya jawo hankalin shugabanni da wakilai daga jihohi 36 na ƙasa, abin da ke nuna muhimmancin taron ga shugabanci da makomar siyasa ta NNPP.

Jagorori kamar su Ajuji Ahmed, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf sun yi bayanai daban-daban a yayin taron da ya samu halartar ƴan jam'iyya.

Wannan taro ya zama wani muhimmin mataki na haɗa kan jam’iyyar da kuma tabbatar da cewa an shirya tsaf domin fafatawa a matakai daban-daban na siyasa.

Addu'ar NNPP ga masu sauya sheka

A baya, mun wallafa cewa Shugaban NNPP, Ajuji Ahmed, ya takaicin yadda wasu ’yan fice daga cikinta zuwa wasu jam’iyyun adawa da mai mulki a Najeriya.

Lamarin ya sa Ahmed ya yi masu fatan tafiyar siyasa mai cike da rudani da kalubale, inda ya bayyana cewa hanyarsu ta ci gaba da zama mai wuyar gaske.

Ahmed ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis, 18 ga Disamba, 2025, yayin taron karo na goma na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da aka gudanar a Abuja,

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng