'Ba Tinubu ba ne,' An Ji Wanda Buhari Ya So Ya Zama 'Dan Takarar APC a zaben 2023

'Ba Tinubu ba ne,' An Ji Wanda Buhari Ya So Ya Zama 'Dan Takarar APC a zaben 2023

  • Babafemi Ojudu ya ce ikirarin da ke cikin littafin Muhammadu Buhari kan takarar Yemi Osinbajo a 2023 ba gaskiya ba ne kuma jita-jita ce marar tushe
  • Sanata Ojudu ya bayyana cewa Buhari ya nuna cikakken goyon baya ga Faresa Osinbajo sau da dama, a sirrance da kuma a bainar jama’a
  • Hadimin ya zargi marubucin littafin da rubuta tarihin da bai cika, ta hanyar gaza tuntubar wadanda suka san gaskiyar abubuwan da suka faru

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mai ba tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shawara kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu, ya fito fili ya karyata ikirarin da ke cikin sabon littafin tarihin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Littafin, mai suna 'Muhammadu Buhari: From Soldier to Statesman', wanda Dr. Charles Omole ya rubuta, ya yi ikirarin cewa Buhari bai mara wa Osinbajo baya a yunkurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Kara karanta wannan

"Yana sane": Diyar Buhari ta fadi halin marigayin da 'yan Najeriya ba su sani ba

Tsohon hadimin Osinbajo ya ce Buhari ya so maigidansa ya zama dan takarar APC a 2023
Yemi Osinbajo tare da Shugaba Bola Tinubu 'yan kwanaki bayan Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa. Hoto: @ProfOsinbajo
Source: Twitter

Ojudu: “Buhari bai hana Osinbajo takara ba”

A cewar littafin, hakan ya faru ne saboda Bola Ahmed Tinubu ma yana cikin masu neman takarar, kuma Buhari yana kallon Tinubu a matsayin uban siyasar Osinbajo, in ji rahoton Punch.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, Ojudu ya bayyana cewa bayanan da ke cikin littafin karya ne kuma sun dogara da jita-jita.

Ojudu ya ce ya kasance cikin wadanda suka saurari tattaunawa da dama tsakanin Buhari da Osinbajo daga shekarar 2016 zuwa 2022, inda suka tattauna kan batun wanda zai gaji shugaban kasa sau da dama.

A cewarsa, a kowanne lokaci Buhari ya bayyana karara cewa Osinbajo na da cikakken ‘yancin yanke shawara kan tsayawa takara.

Ya ce a wata tattaunawa, Buhari ya bukaci Osinbajo ya yi tunani sosai game da kudurinsa na yin takara, sannan ya tabbatar masa da cewa duk shawarar da ya dauka zai goyi bayansa.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: 'Yar Buhari ta fadi yadda ake amfani da sa hannun marigayin

“Osinbajo shi ne ya fi dacewa” – Buhari

Ojudu ya kara da cewa a tattaunawa ta uku, Buhari ya bayyana Osinbajo a matsayin mutumin da ya fi dacewa da shugabancin Najeriya, yana mai nuni da kwarewarsa, biyayyarsa, da rawar da ya taka wajen tafiyar da gwamnati.

A cewarsa, Buhari ya jaddada cewa Osinbajo ya riga ya san sirrin tafiyar da gwamnati, kuma ya nuna kwazo da nutsuwa a lokutan da ya rike mukamin mukaddashin shugaban kasa.

Ojudu ya ce ko da kafin a sayi fom din takarar shugaban kasa a madadin Osinbajo, Buhari ya sake tabbatar da cikakken goyon bayansa, ba tare da wani shakku ba.

Ojudu ya ce sau tari Buhari ya nuna cewa Osinbajo ya cancanci shugabancin Najeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari (marigayi) da Yemi Osinbajo a lokacin suna kan mulki. Hoto: @ProfOsinbajo
Source: Facebook

Goyon baya a bainar jama’a da sukar littafin

Ojudu ya bayyana cewa goyon bayan Buhari bai tsaya a maganganun sirri ba kamar yadda jaridar PM News ta rahoto.

Ya ce Buhari ya yaba wa Osinbajo a bainar jama’a a wani taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), tare da ba shi shawarwari kan yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Labarin tsohon sakataren Buhari da ministoci da mukarraban gwamnati ke shakka

Ya kuma zargi marubucin littafin rayuwar Buhari da rashin tuntubar muhimman mutane da suka san gaskiyar abubuwan da suka faru, yana mai cewa littafin ya karkata ga bangare guda, wanda bai wakilci cikakken tarihin lamarin ba.

El-Rufai ya yi magana kan littafin Buhari

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamna, Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su bar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya huta lafiya.

Ya yi gargadi game da kokarin tayar da rikici, rarrabuwar kai ko anfani da tarihinsa don cimma wasu bukatun siyasa da jawo maganganu a tsakanin 'yan Najeriya.

El-Rufa’i ya ce taron kaddamar da littafi a kan tsohon shugaban kasa ya tayar masa da hankali, ganin yadda aka sake nuna tsofaffin rarrabuwar kai da ke kewaye da Buhari tun yana raye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com