Sarki Ya Hada Tawaga Zuwa wajen Tinubu, Sun Goyi bayan Tazarcensa a 2027
- ’Yan yankin Ogbia daga jihohin Bayelsa da Rivers sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Sun ce salon jagorancinsa na haɗa kai da kuma ayyukan raya yankin Neja-Delta ne ya sanya su suka dauki wannan matsaya
- Tawagar dattawan ta kuma miƙa buƙatu na musamman, ciki har da kafa cibiyar nazarin makamashi da man fetur a Ogbia
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Wasu sarakunan gargajiya daga masarautar Ogbia, wadda tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya fito, sun yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya sake neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.
Sun bayyana hakan ne a daren Laraba yayin wata ziyarar godiya da suka kai wa Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai game da ziyarar da suka kai fadar shugaban kasa ne a wani bidiyo da hadimin Tinubu, Dada Olusegun ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Ogbia ya yaba wa Bola Tinubu
Tawagar wadda Sarkin Ogbia, Obanobhan III, Sarki Dumaro Charles Dwaba, ya jagoranta, ta ce shugaba Tinubu ya nuna kulawa ga ’ya’yan Ogbia ta hanyar naɗa su a muƙamai masu muhimmanci.
A jawabin da Sarki Collins Daniel ya karanta a madadin tawagar, an ce masarautar Ogbia za ta ba shugaban ƙasa cikakken goyon baya domin ganin an gina Najeriya.
Rahoton Vanduard ya nuna cewa sun jaddada cewa goyon bayan nasu ya samo asali ne daga abin da suka gani a aikace ba tare da tilas ba.
Tinubu na kan daidai inji Sarkin Ogbio
’Yan Ogbia sun bayyana goyon bayansu ga manufar 'Renewed Hope' ta shugaba Tinubu, suna cewa manufofin sun sake farfaɗo da lamura a yankin Neja-Delta.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023
Sun ce naɗe-naɗen da aka yi wa ’ya’yan yankin sun ƙarfafa musu gwiwa da amincewa da gwamnatin tarayya karkashin Tinubu.
Daga cikin mutanen da suka ambata an ba mukamai akwai Alƙali Moore Abraham Aseima Adumein na Kotun Ƙoli, shugaban hukumar NDDC, Dr Samuel Ogbuku.
Saura sun hada da Sir Tonye Okio, da mai ba shugaban ƙasa shawara kan shari’a da fasahar zamani, Barrista Fernandez Marcus-Obiene.

Source: Twitter
Rokon 'yan Ogbia ga shugaba Tinubu
’Yan Ogbia sun tunatar da gudunmawar yankin a tarihin Najeriya, musamman gano man fetur a Oloibiri a 1956, wanda ya sauya tsarin tattalin arziƙin ƙasar.
Sun kuma ambaci rawar da yankin ya taka wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa, ciki har da sadaukarwar Goodluck Jonathan a 2015.
A dalilin haka, sun buƙaci a ba Ogbia kulawa ta musamman ta hanyar kafa cibiyar nazarin makamashi da man fetur, da kuma kare yankunan bakin teku daga zaizayar ƙasa.
A ƙarshe, sun tabbatar wa shugaba Tinubu da cikakken goyon baya tare da yi masa fatan samun lafiya wajen jagorantar Najeriya.
Shugaba Tinubu zai yi tazarce inji Umahi
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan ayyuka na tarayya, Dave Umahi ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai yi tazarce a 2027.
Umahi ya ce a halin da ake ciki, shugaban kasar ba shi da fargaba ko dar-dar game da goyon bayan 'yan Kudu maso Gabas.
Ministan ayyukan ya yi magana ne bayan wani Sanata daga yankin ya ce shugaban kasar zai sha kaye a zaben 2027 mai zuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

