Gwamna Makinde Ya Ba da Tabbaci kan Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

Gwamna Makinde Ya Ba da Tabbaci kan Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya gabatar da jawabai a wajen kaddamar da wani littafin da Lai Mohammed ya wallafa
  • A yayin jawabinsa, Gwamna Makinde ya tabo batun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya
  • Gwamna Makinde ya kuma bayyana wasu 'yan siyasa na kawo dabarun rarraba kawunan 'yan kasa domin cimma muradunsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya karyata rade-radin da ke cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Gwamna Makinde ya jaddada cewa yana nan daram a PDP duk da ficewar wasu gwamnonin adawa zuwa APC a baya-bayan nan.

Gwamna Makinde zai ci gaba da zama a PDP
Gwamna Seyi Makinde na jawabi a wajen taro Hoto: @seyimakinde
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da wani littafi a ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2025 a Abuja.

Kara karanta wannan

"Ba zan taba komawa APC ba," Sanata ya yi kaca kaca da gwamnoni 6 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya wallafa littafin mai taken “Headlines and Soundbites: Media Moments that Defined an Administration”.

Me Makinde ya ce kan komawa APC?

Gwamna Makinde ya bayyana cewa bai da niyyar sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

“Ni ba dan APC ba ne, kuma ba ni da niyyar zama dan APC."

- Gwamna Seyi Makinde

Gwamna Makinde ya yi muhimman jawabai

Ya ce cigaban Najeriya na bukatar hadin gwiwa ta gaskiya tsakanin shugabanni daga bangarorin siyasa daban-daban domin ciyar da kasar gaba.

Gwamnan ya yi nuni da cewa rarrabuwar kawuna da ke kara tsananta a Najeriya na fitowa ne daga burin manyan ’yan siyasa, ba daga muradin talakawa ba.

A cewarsa, yawancin ’yan Najeriya na bukatar hadin kai da zaman lafiya, amma galibi ana amfani da su ana rarraba su ta fuskar addini, kabila da yanki, sakamakon manufofin wasu ’yan siyasa masu neman cimma bukatun kansu.

Kara karanta wannan

Gwamna Aiyedatiwa ya fadi dalilin da ya sa gwamnonin PDP ke komawa APC

Gwamna Makinde ya ce Najeriya na bukatar yarjejeniya a tsakanin masu fada a ji wadda za ta mayar da hankali kan inganta shugabanci da magance kalubalen zamani, maimakon ci gaba da tona tsofaffin sabani.

Gwamnan jihar Oyo ya tuna baya

Da yake magana kan abubuwan da ya gani a baya, gwamnan ya ce nasarar siyasa a karshe tana hannun Allah da kuma lokaci.

Gwamna Makinde ya ce ba zai koma APC ba
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: @seyimakinde
Source: Facebook

Gwamna ya tuna baya kan yadda manyan ’yan siyasa, ciki har da shi kansa da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, suka sha faduwa a zabubbuka a lokuta daban-daban kafin daga bisani su samu nasara bayan shekaru.

Makinde ya kuma waiwayi kalubalen tarihi da Najeriya ta fuskanta, yana mai bayyana cewa yayin da shugabannin farko suka fi mayar da hankali kan hada kan kasa bayan yakin basasa, matsalolin yau sun bambanta kuma suna bukatar sababbin hanyoyin warwarewa.

Ya yi kira da a yi gagarumin yunkuri wajen tsara tsare-tsaren siyasa da na shugabanci da za su inganta adalci, shigar da kowa cikin lamarin kasa da kuma dorewar zaman lafiya.

Sanatan PDP ya koma jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta gamu da babban koma baya a majalisar dattawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Kefas: Gwamnan da fice daga PDP kwanan nan ya yanki katin zama ɗan jam'iyyar APC

Sanata Sunday Marshall Katung mai wakiltar Kaduna ta Kudu ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Sunday Marshall Katung ya bayyana cewa PDP ta samu kanta cikin tsaka mai wuya saboda rarrabuwar kawuna, wanda hakan ya tilasta masa neman mafita.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng