Ana Ganin Kwankwaso da Gwamna Abba Za Su Koma APC, Ganduje, Barau Sun Fara Shiri

Ana Ganin Kwankwaso da Gwamna Abba Za Su Koma APC, Ganduje, Barau Sun Fara Shiri

  • Jita-jitar da ake yadawa game da yiwuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da Rabiu Musa Kwankwaso za su koma APC ta kara dawowa
  • Masana sun ce sauya shekarsu zai rikita lissafin APC a Kano, musamman game da burin Sanata Barau Jibrin na yin takarar gwamnan jihar a 2027
  • Yayin da wasu ke ganin cewa APC za ta kara karfi idan Abba da Kwankwaso suka koma jam'iyyar, wasu kuma na ganin abin ba mai yiwuwa bane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano — Duk da cewa babu wata takamaimiyar hujja, jita-jitar ta kara karfi game da yiwuwar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da jagoransa a siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso, za su koma jam’iyyar APC.

Masana da masu sharhi kan siyasa na ganin cewa idan hakan ta faru, matakin zai iya girgiza siyasar Kano tare da sake fasalin jam’iyyun jihar kafin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Fubara, Adeleke da wasu gwamnoni 3 da suka fice daga jam'iyyar PDP a shekara 2

Jita-jitar Kwankwaso da Abba za su koma APC a Kano zai tayar da jijiyoyin wuya
Gwamna Abba Yusuf da Sanata Rabiu Kwankwaso da ake zargin za su koma APC a Kano inda Barau Jibrin ke shirin yin takara. Hoto: @KwankwasoRM, @barauijibrin
Source: Twitter

Jawabin Kwankwaso kan yiwuwar shiga APC

Jita-jitar ta fara karfi ne a watan Satumba, 2025 lokacin da Kwankwaso, wanda aka fi sani da Madugu, ya lissafo wasu “tsauraran sharudda” da dole APC ta cika kafin ya amince da komawa jam’iyyar, kamar yadda Arise News ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin tarbar wasu sababbin masu sauya sheka 45, Kwankwaso ya ce zai dawo APC ne kawai idan jam’iyyar ta fayyace tagomashin da NNPP za ta samu.

Sanata Kwankwaso ya ce:

“Za mu iya komawa APC amma bisa sharudda. Ba za mu shiga mu bar wani yana juya mu ba. Dole a fada mana abin da NNPP za ta amfana daga wannan hadaka.”

Maganganun nasa sun kara tayar da hazo a tsakanin manyan APC a Kano, domin wasu da dama daga cikinsu sun wasa wukakensu domin neman tikitin gwamnan jihar a 2027.

Tasirin komawar Abba da Kwankwaso APC

Kara karanta wannan

"Ka jefa kanka a matsala": PDP ta zargi Gwamna Fubara da rauni bayan komawa APC

Idan har Abba da Kwankwaso suka koma jam'iyyar, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, tambayar farko ita ce: shin wa zai zama jagoran APC a Kano?

A halin yanzu, tsohon gwamna kuma tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, shi ne ake ganin jagoran APC a Kano. Amma masana na ganin cewa shigowar Kwankwaso da Abba zai iya rikita wannan tsari.

Babbar damuwa ta biyu ita ce takarar 2027 ta mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin. Yanzu haka ana rade-radin cewa Barau na neman kujerar gwamna.

Amma idan Abba ya koma APC, wasu na ganin jam’iyyar za ta iya bashi “takara saboda kasancewarsa gwamna mai ci, kuma mai rike da madafun iko”, lamarin da ka iya rusa shirin Barau.

Wasu jiga-jigan APC sun yi gargadin cewa idan Abba ya samu tikitin takara a APC, masu shirin takara na yanzu za su iya ficewa daga jam'iyyar ko kuma su yi tawaye.

Me ‘yan siyasa ke cewa kan wannan lamari?

Kamalu Bako Lamido, tsohon hadimin Ganduje, ya ce “Abba ba zai taba shiga APC shi kadai ba”, yana mai cewa hakan zai datse alakarsa da Kwankwaso tare da karin karfin Ganduje.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro Ganduje kan ƙoƙarin yi wa Hisbah kishiya a Kano, an ja layi

Sai dai wani masanin siyasa, Dr. Kabiru Sufi, ya ce komawar Abba da Kwankwaso APC da ake magana a kai abu ne mai yiwuwa, amma ya jam'iyyar cewa dole ta yi lissafi sosai don kauce wa barakar cikin gida.

A nasa bangaren, Zilyadaini Mustapha Karaye, wanda ya kasance makusancin Ganduje, ya ce ko Abba da Kwankwaso sun shiga APC, Barau Jibrin ne zai fi rinjaye musamman idan jam’iyyar ta yi zaben fitar da gwani na kato bayan kato.

Zilyadaini Mustapha Karaye, ya ce:

“Ko da sun koma jam'iyyar APC kamar yadda ake tunani, ra'ayin wakilan zabe mafi rinjaye ne zai yanke wanda zai yi takara, wani cewa shi gwamna ne ba zai yi tasiri ba."
Siyasar jihar Kano za ta dauki zafi sosai idan Abba Yusuf da Kwankwaso suka koma APC.
Taswirar jihar Kano, inda ake zargin Gwamna Abba da Kwankwaso za su koma APC. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kano: Yiwuwar barkewar rikici a jam'iyyar APC

Wani masanin siyasa, Adamu Aminu Fagge ya yi gargadin cewa APC a jihar Kano na fuskantar baraka tun yanzu, domin wasu masu sha’awar mulki suna kashe kudi don karfafa kansu.

Ya ce:

“Wasu ‘yan siyasa, musamman wakilan zabe, har ma da masu sha'awar takarar ba su da tsayayyen bangare. Duk wanda zai bude masu aljihu su kwashi rabonsu ne zai samu goyon bayansu a karshe."

Kara karanta wannan

'Hisbar Ganduje za ta jawo hallaka rayuka a Arewa,' Tsohon kwamishina ya yi gargadi

Masana na cewa idan Abba da Kwankwaso sun koma APC, jam’iyyar za ta samu karfi amma kuma lamarin zai iya tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin wadanda ke da muradin yin zabe tun farko.

'APC na neman taimakon Kwankwaso' - NNPP

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya cika baki game da karfin siyasar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Hashimu Dungurawa ya zargi APC da rikicewa tare da neman tallafin Kwankwaso, yana mai cewa NNPP yanzu ta shahara, kuma zabukan 2027 za su zama daban.

A cewar shugaban jam'iyyar mai mulki a Kano, ’yan jam'iyyar APC sun rikice kuma sun san ba tare da Kwankwaso ba, ba za su yi nasara a zaben 2027 ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com