ADC Za Ta Yi Babban Kamu, Mataimakin Gwamna da Sanata Sun Shirya Ficewa daga PDP
- Jam'iyyar PDP na shirin sake samun koma baya a jihar Bayelsa 'yan watanni bayan ficewar Gwamna Douye Diri zuwa APC mai-ci
- Majiyoyi sun nuna cewa mataimakin gwamnan jihar da Sanata Seriake Dickson sun shirya tattara 'yan komatsansu daga jam'iyyar PDP
- Ana ganin cewa shirye-shirye sun yi nisa kan jam'iyyar da manyan 'yan siyasar biyu za su koma domin tunkarar zaben shekarar 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bayelsa - Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo, da Sanata Seriake Dickson na dab da barin PDP.
Majiyoyi sun ce Lawrence Ewhrudjakpo da tsohon gwamna kuma sanata mai ci, Seriake Dickson, na shirin ficewa daga jam'iyyar PDP.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa wannan yunkuri na da nasaba da rikice-rikicen shugabanci da rashin tabbas da ke damun jam’iyyar PDP a matakin kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC za ta yi babban kamu a Bayelsa
Yayin da Sanata Dickson ya kasance mai sukar APC sosai a majalisar dattawa, Ewhrudjakpo ya ki bin Gwamna Douye Diri, wanda ya koma APC a ranar 3 ga watan Nuwamban 2025.
A yanzu ana ganin su duka biyun sun fara tattaunawa da jam'iyyar ADC domin sabuwar mafaka ta siyasa.
Ana kyautata zaton cewa Dickson zai yi amfani da ADC domin komawa majalisar dattawa, yayin da Ewhrudjakpo kuma zai yi amfani da jam’iyyar wajen tsayawa takarar gwamna.
Dangane da shirin sauya shekar Sanata Dickson da Ewhrudjakpo, wata majiya daga ofishin gwamnan jihar ta ce akwai kamshin gaskiya a ciki.
Majiyar ta ce jita-jitar na kara yaduwa ne saboda Dickson na da alaka da ADC, inda ta kara cewa ya taka rawar gani wajen ba wasu 'yan siyasa a jihar mukamai a jam'iyyar.
Sannan ta ce babu dalilin da zai sa ta yi shakkun cewa Dickson da mataimakin gwamna za su koma jam'iyyar ADC.
Ana ganin ADC ba ta da karfi a Bayelsa
Sai dai, ta ce ADC ba za ta iya yin nasara ko a karamar hukuma daya ba saboda ba ta samu karbuwa ba a jihar.

Source: Facebook
Wani kusa da Gwamna Diri ya ce:
“Kowane ɗan siyasa yana son ci gaba, kuma dole ne ya tsaya takara a wata jam’iyya. Amma yadda PDP ke tafiya, dole Dickson zai fice. Ni ina ganin zai bi gwamna ya koma APC. ADC ba zaɓi ba ce, duk wanda ya tafi can ya yi kuskure."
Sai dai, ya ce duk da haka Dickson na iya komawa ADC ne saboda sake tsayawa takarar sanata karo na uku saboda zai sha wuya idan ya tsaya a PDP.
Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Doubara Otasi, ya ce bai san matakin da ubangidansa zai dauka ba a yanzu.
Gwamna Adeleke ya magantu kan barin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi tsokaci kan dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP.
Gwamna Adeleke ya bayyana cewa yana matukar kaunar PDP amma dole ce ta sanya ya tattara 'yan komatsansa ya fice daga cikinta.
Ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar AP ne bayan ya fahimci cewa rikicin da ya addabi PDP ba mai karewa ba ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


