Tirkashi: Tsohon Minista Ya Jefar da Tsintsiya, Ya Sauya Sheka daga APC zuwa PDP

Tirkashi: Tsohon Minista Ya Jefar da Tsintsiya, Ya Sauya Sheka daga APC zuwa PDP

  • Tsohon ministan kwadago Joel Ikenya ya sanar da ficewarsa daga APC zuwa PDP, bayan dogon nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki
  • Ikenya, wanda ya taba rike mukamai daga majalisar jiha zuwa majalisar tarayya, ya ce PDP ce jam’iyyar da ta gina siyasar sa tun farko
  • Sauya shekar ta zo ne a daidai lokacin da Gwamna Agbu Kefas ke shirin komawa APC, lamarin da ya tayar da muhawara a siyasar Taraba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba - A wani yanayi na ban mamaki, tsohon ministan kwadago, Sanata Joel Danlami Ikenya, ya yi murabus daga zama mamban jam'iyyar APC mai mulki a kasa.

Sanata Joel Ikenya, tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Taraba ta Kudu daga 2007 zuwa 2011 ya koma jam'iyyar PDP bayan barin APC.

Kara karanta wannan

"Ka jefa kanka a matsala": PDP ta zargi Gwamna Fubara da rauni bayan komawa APC

Tsohon ministan kwadago, Joel Danlami Ikenya ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.
Tsohon ministan kwadago, kuma tsohon sanatan Taraba, Joel Danlami Ikenya da ya fice daga APC zuwa PDP. Hoto: @SenIkenya
Source: Twitter

Tsohon minista ya fice daga APC zuwa PDP

Dan majalisar dattawan ya fice daga APC ne yayin da Gwamna Agbu Kefas ya shirya komawa jam'iyyar bayan barin PDP, a cewar rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya sanar da sauya shekarsa daga APC zuwa PDP ne a cikin wata wasika mai taken, 'Sanarwar sauya sheka daga Sanata Joel Danlami Ikenya,' wacce aka rabawa manema labarai a Jalingo.

A cikin wasikar, tsohon ministan ya ce ya dauki wannan mataki mai girma ne bayan "dogon nazari, tattaunawa mai zurfi, da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki."

Ya kuma kara da cewa:

"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa na sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP bisa radin al'umma ta, da jihar Taraba."

Sakon tsohon minista ga magoya bayansa

Ya jaddada cewa jam'iyyar PDP ta kasance wani ginshiki ga ci gaban siyasarsa kuma ba zai so ya yi watsi da jam'iyyar da ta goya shi a lokacin da yake bukatar hakan ba.

Kara karanta wannan

Awanni 24 bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Fubara ya fice daga PDP zuwa APC

"Na san da yawanku suna sane da cewa PDP ta kasance jam'iyyar da ta ba ni damar da na cimma gaci a siyasa ta, na taka manyan mukamai, kuma ina ga, nan ne ya kamata na dawo na zauna yanzu."

- Sanata Joel Danlami Ikenya.

Ya nuna matukar godiyarsa ga daukacin masoya da magoya bayansa bisa irin "kauna da goyon bayan" da suka nuna masa tsawon lokacin da yake wakiltar su, in ji rahoton Premium Times.

Sanata Ikenya, wanda ya kasance a jam'iyyar PDP na tsawon lokaci, ya zama wata fitila a siyasar Taraba, musamman Wukari da kudancin Taraba, inda ya fi karfi.

Sanata Danlami Ikenya ya fice daga jam'iyyar APC zuwa PDP.
Tsohon ministan kwadago Joel Danlami Ikenya da ya fice daga APC zuwa PDP. Hoto: @SenIkenya
Source: Twitter

Ikenya: Bayani a kan siyasar tsohon minista

Rahoto ya nuna cewa Sanata Ikenya ya fara siyasarsa ne a matsayin dan majalisar dokokin jihar Taraba daga 19999 zuwa 2003, sannan ya tsallaka zuwa majalisar wakilai daga 2003 zuwa 2007, kuma ya kara gaba zuwa majalisar dattawa daga 2007 zuwa 2015, duka a karkashin jam'iyyar PDP.

Ya zama ministan kwadago da inganta ayyuka a karkashin gwamnatin shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, mukamin da ya rike daga Maris zuwa Mayun 2015.

A cikin wasikar, Sanata Ikenya ya tabbatar wa masoyansa cewa dawowarsa jam'iyyar PDP na da nasaba da kudurinsa na yi wa al'ummarsa hidima yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya gaji da rikicin PDP, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Gwamna Kefas ba zai shiga APC a 2025 ba

A wani labarin, mun ruwaito cewa, za a gudanar da gagagrumin bikin sauya shekar Gwamna Agbu Kefas zuwa jam'iyyar APC a watan Janairu, 2026.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Taraba, Ibrahim Tukur, ya ce jam'iyyar ta ga dacewar sauya lokacin taron zuwa Janairu saboda bukukuwan Disamba.

Ibrahim Tukur ya kuma sanar da cewa APC ta dakatar da wasu shugabanni a matakin gunduma saboda karya dokokin gudanarwar jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com