'Da Lauje cikin Naɗi': Atiku Ya Yi Mamaki da Tinubu Ya Naɗa Tsohon Shugaban INEC Jakada

'Da Lauje cikin Naɗi': Atiku Ya Yi Mamaki da Tinubu Ya Naɗa Tsohon Shugaban INEC Jakada

  • Atiku Abubakar ya soki nadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, a matsayin jakada
  • Ya ce da shi ne shugaban ƙasa, babu abin da zai sa ya yi wa wanda ya jagoranci babban zaɓen da aka yi ta cece-kuce naɗi
  • Atiku ya yi gargadin cewa wannan na iya zama kamar lada ne ba bisa cancanta ba, kuma hakan zai iya lalata martabar zaben Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka kan matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na naɗin jakada daga hukumar zaɓe INEC.

Atiku, wanda tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa ne a ƙarƙashin PDP ya ce nadin tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, domin zama jakada zai aika sako mata kyau ga duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi bayani game da 'rabon' motocin yi wa Tinubu kamfen

Atiku ya yi takaicin nada tsohon Shugaban Hukumar zabe mukami
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, Farfesa Mahmoud Yakubu, Shugaba Bola Tinubu Hoto: Atiku Abubakar/Plateau Update/Bayo Onanuga
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku, ya ce wannan mataki ba wani abu ne da zai taɓa yi ba idan shi ne shugaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya soki Tinubu kan naɗin jakada

A cewar Atiku, wannan abu da Shugaba Bola Tinubu ya yi, za a iya fassara shi a matsayin bayar da lada, amma ba wai an yi naɗin saboda cancanta ba.

Ya ƙara da cewa tun da gwamnatin Tinubu na fama da matsalolin sahihancin ta fuskoki da dama, bai kamata ta ƙara ɗora kanta a irin wannan zargi ba.

Atiku ya ce:

“Babu wani yanayi da a matsayina na Shugaban Ƙasar Najeriya, zan naɗa tsohon shugaban INEC a matsayin jakada.”

Atiku ya fadi illar nadin tsohon Shugaban INEC

A cewar tsohon ɗan takarar, wannan mataki na iya nuna kamar ana ba da lada ne kan yadda aka gudanar da zaɓen 2023, wanda har yanzu ake ta mahawara a kai.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya samu kariya ana tsaka da kiran Tinubu ya kore shi

Atiku ya yi nuni da cewa hakan na iya aika saƙo mara kyau ga shugabannin INEC na yanzu, inda za su iya ɗauka cewa zabe mara inganci, na iya zama hanyar samun mukamin gwamnati.

Atiku ya ce nadin Mahmoud Yakubu kamar bayar da ladan aikin zabe ne
Tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya ce:

“Ba daidai ba ne a nada wanda ya jagoranci zaɓen da aka yi ta cece-kuce akansa."

Ya ce hakan ba zai taimaka wajen gina dimokuraɗiyya ba, kuma zai ƙara dagula amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati, musamman na gudanar da zaɓe.

A halin yanzu dai, nadin da Shugaba Tinubu ya yi wa Mahmood Yakubu a matsayin jakada yana gaban majalisar dokoki domin tantancewa da amincewa.

Atiku ya gana da manyan ADC

A baya, mun wallafa cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya sa labule da manyan ADC.

Atiku, wanda ya taba neman kujerar Shugaban Ƙasa a Zaben 2023 ya karɓi shugabannin jam’iyyarsa na jihohi 36 da na Abuja a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Shugabannin ADC sun kai ziyarar ne ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar na Jihar Kogi, Ogga Kingsley, inda suka tattauna da Atiku kan makomar siyasa da babban zaɓen 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng