Bayan An Ceto Daliban Kebbi, Ƴan Siyasa fiye da 1500 Sun Fice daga PDP zuwa APC

Bayan An Ceto Daliban Kebbi, Ƴan Siyasa fiye da 1500 Sun Fice daga PDP zuwa APC

  • Manyan jiga-jigan PDP sama da mutum 1,500 daga masarautar Zuru sun koma APC a Birnin Kebbi, suna danganta sauyawar da rawar da Gwamna Nasir Idris ke takawa
  • Shugaban APC na jihar Kebbi, Abubakar Kana-Zuru, ya ce ayyukan hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi da tsaro sun kara tabbatar da amincin jama’a ga gwamnatin yanzu
  • Manya da matan da suka sauya sheka sun ce PDP ta rasa tasiri a yankin, suna alkawarin cewa Danko-Wasagu da Zuru za su kawo kuri'u cikakku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - A wani babban taron da ya girgiza siyasar Kebbi, fiye da mambobin PDP 1,500 daga yankin Zuru sun sanar da sauya shekarsu zuwa jam’iyyar APC.

Taron, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, ya ja hankalin jama’a da dama saboda yawan mutanen da suka bar jam’iyyar adawa lokaci guda.

Kara karanta wannan

Duniya na kallo: Harin Kebbi da wasu hare hare da suka girgiza Arewa a Nuwamba

APC ta kara karfi a Kebbi, fiye da mutane 1,500 sun shiga jam'iyyar daga PDP
Wani gangamin jam'iyyar APC da aka gudanar a mazabar Ganye, jihar Adamawa. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Mutane 1,500 sun bar PDP zuwa APC

Wannan sauyin sheka ya kara hargitsa yanayin siyasar Kebbi gabanin zabukan jihar da ke tafe, a cewar rahoton jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake karɓar sababbin mambobin, shugaban APC na jihar, Alhaji Abubakar Kana-Zuru, ya ce wannan sauyi ya faru ne saboda ayyukan Gwamna Nasir Idris da suka tabo rayuwar jama’a kai tsaye.

Ya ce ayyukan hanyoyi da tituna, gyaran asibitoci, sabunta cibiyoyin kiwon lafiya, da gyaran makarantun firamare da sakandare a sassa daban-daban na jihar ne suka jawo ra'ayin mutane.

A cewarsa, aikin hanyar Koko–Dabai–Zuru kadai ya isa ya tabbatar wa jama’a cewa Gwamna Nasir Dr. Idris ya cancanci a zabe shi a wa'adi na biyu.

Dalilin sauya shekar jiga-jigan PDP a Kebbi

Tsohon dan takarar majalisar Kebbi, Alhaji Lawali Arzika Riba, ya yi magana mai zafi game da sauya shekarsu, yana mai cewa PDP ta gaza rike amanar jama'a.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamna Nasir ya ba daliban da 'yan bindiga suka saki a Kebbi

Hon. Lawali ya ce Gwamna Idris ya nuna babbar jajircewa ta musamman wajen hadin kai da hukumomin tsaro a lokacin ceto daliban GGCSS Maga da aka sace.

A cewarsa, irin wannan aiki da gwamnatin APC a jihar ta gudanar ya jawo ra'ayinsa zuwa jam'iyyar tare da daukar matakin barin PDP, in ji rahoton Daily Post.

Wadanda suka sauya shekar sun ce Gwamna Nasir Idris ya cancanci ya samu tazarce.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris a wajen wani taro a Birnin Kebbi. Hoto: @KBStGovt
Source: Facebook

'Danko-Wasagu ya zamo sansanin APC' - Mata

Matan yankin Danko-Wasagu, Binta Bena da Hajiya Maryam, sun bayyana cewa PDP ta ruguje a yankinsu sakamakon rashin tsari da rashin tasirinta.

Sun ce Gwamna Idris ya nuna shugabanci na gaskiya wanda ya sa suka yanke shawarar barin PDP domin su yi aiki tare da APC. A cewarsu, yankinsu zai kawo kuri’u masu yawa ga APC a zaben da ke tafe.

Gagarumin sauyin jam’iyya daga PDP zuwa APC ya kara karfin siyasa ga gwamnatin jihar, musamman a yankin Zuru da Danko-Wasagu da ke da yawan masu kada kuri'a.

Magoya bayan APC sun koma PDP a Jigawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fiye da 'yan siyasa 1,600 da ke goyon bayan jam'iyya mai mulki ta APC a jihar Jigawa sun sauya sheƙa zuwa PDP.

Kara karanta wannan

An kashe mutum 2 da ƴan bindiga suka je sace dalibai a Kogi? Gwamnati ta yi martani

Wadannan 'yan siyasar 1,6000 sun fice daga APC zuwa PDP a wani gagarumin gangami da aka gudanar a Limawa, karamar hukumar Dutse.

Matasa, maza da mata daga yankuna daban-daban na Limawa sun hallara da tutar PDP, inda suka bayyana cewar sun gaji da “alkawuran APC da ba a taɓa cika wa ba.”

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com