Jira Ya Kare: Atiku Ya Sa Lokacin Zama Dan Jam'iyyar ADC bayan Ya Dade da Barin PDP
- Ana sa ran Atiku Abubakar zai yi rajistar zama cikakken mamban ADC yau, wanda zai sauya siyasar Najeriya gabanin 2027
- 'Dan takarar shugaban kasar ya ce sabon burin sauya Najeriya ne ya kai su ADC, inda ya nemi al’umma su shiga jam'iyyar
- A watan da ya wuce, kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana dalilin da ya jawo jinkirin Atiku na zama mamban jam'iyyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, yana shirin zama cikakken mamban jam’iyyar ADC a yau Litinin.
Wata majiya da ke kusa da shi ta tabbatar da cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin Atiku ya yi rajistar shiga ADC a Jada Ward 1, jihar Adamawa, inda ya fito.

Source: Twitter
'Gobe zan zama cikakken mamba' - Atiku ga ADC
A wata ganawa da ya yi da shugabannin ADC na Adamawa a Yola, Atiku ya yi karin haske kan matakin, yana mai cewa burin kawo sauyi a Najeriya ya kai su ga kaddamar da ADC, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi ga shugabannin jam’iyyar, Atiku ya ce:
“A yau, a Najeriya, akwai sabuwar gwagwarmayar siyasa, ko ba haka ba? Yau wannan gwagwarmayar ina ta kai mu? Ta kai mu ADC. Don haka mutanen Adamawa da Najeriya, sabuwar jam’iyyarmu ita ce ADC.”
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya nemi shugabannin ADC su shirya karɓarsa, inda ya ce:
“Gobe zan zama cikakken mamba. Kun shirya karɓa ta?”
Wannan tambaya ta jawo babbar amsa ta “Eh!” daga mahalarta taron.
Abin da ya jawo jinkirin shigar Atiku ADC
Tun bayan da hadakar adawa da Atiku da Peter Obi ke jagoranta ta amince da ADC a watan Yuli domin takarar shugaban kasa a 2027, mutane da dama na tambaya ko shugabannin biyu za su shiga jam’iyyar a ko a'a.
A watan da ya wuce, kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ba su da katunan mambobi da suka dace, shi ya jawo jinkirin shigar su Atiku ADC.
Ya ce:
“Katunan da muka zo muka tarar ba su da inganci. Sababbin katunan da shugaban jam’iyya David Mark da sakataren jam’iyya Rauf Aregbesola suka sanya hannu su ne kadai ingantattu.”

Source: Twitter
Aregbesola ya fara sabuwar rajista a Osun
A ranar 19 ga Nuwamba, 2025, Aregbesola ya sanar da fara sabuwar rijista ta jam’iyyar, yana mai cewa shi ma ya yi rajistarsa a Ward 8, Unit 1, Ifofin, Ilesa ta Gabas, jihar Osun.
Ya yi kira ga tsofaffin mambobin jam'iyyar da su sabunta rajistarsu, sababbi kuma su shiga jam’iyyar yanzu, in ji rahoton Punch.
Shigowar Atiku yau, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, na iya zama daya daga cikin manyan abubuwan da za su girgiza siyasar Najeriya kafin 2027.
Sabuwar rigima ta kunno kai a ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsugunne ba ta kare ba kan rikicin shugabanci da ake fama da shi a jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya.
Wani bangare na jam'iyyar karkashin jagorancin Nafiu Bala, ya aika da gargadi ga Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran 'yan hadaka.
Hakazalika, bangaren ya soki hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan amincewa da shugabancin Sanata David Mark.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


