Ba Ja da baya: Malami Ya Ayyana Shiga Takarar Kujerar Gwamnan Kebbi a Zaben 2027

Ba Ja da baya: Malami Ya Ayyana Shiga Takarar Kujerar Gwamnan Kebbi a Zaben 2027

  • Tsohon ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kebbi a zaben 2027
  • Malami ya soki gwamnatin jam’iyyar APC, inda ya ce ta jawo karuwar tsadar rayuwa da gaza magance matsalar tsaro
  • Tsohon ministan ya ce yana da yakinin zai samu nasara a zaben, saboda al'umma suna sonsa, kuma zai kawo masu sauyi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan Najeriya, Abubakar Malami, ya tabbatar da cewa zai shiga tseren gwamnan Jihar Kebbi a 2027.

Ya bayyana cewa kiraye kirayen da jama'a suka dade suna yi ne ya amsa kiransu yanzu, duk da cewa lokacin fara gangamin siyasa bai yi ba a halin yanzu.

Abubakar Malami ya ayyana shiga tseren gwamnan Kebbi a zaben 2027.
Hoton tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami. Hoto: @ADCVanguard_/X
Source: Twitter

Malami zai shiga tseren gwamnan Kebbi

Abubakar Malami ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar watsa labarai ta DCL Hausa.

Kara karanta wannan

Alaka ta yi tsami tsakanin Tinubu da Yahaya Bello? An ji gaskiyar zance

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malami ya tabbatar da cewa ya yanke shawara fitowa neman kujerar gwamnan jihar Zamfara a 2027, kuma babu abin da zai sanya ya ja da baya.

Ya ce yana da yakinin samun nasara saboda jama’a sun nuna cikakken goyon baya gare sa, kuma kiraye-kirayensu ne ma ya sa zai fito takarar.

Yayin da ya zai fafata a 2027, tsohon ministan ya soki gwamnatin APC a jihar, yana mai cewa tsare-tsaren gwamnati sun kara jefa yankin Arewa cikin wahala

A cewarsa, matsalolin tsaro sun mayar da manoma baya, abin da ya haifar da rufewar kamfanonin sarrafa shinkafa da suke aiki na tsawon shekaru 20.

Dalilan Malami na neman gwamnan Kebbi

Malami ya bayyana cewa burinsa shi ne ceto jihar Kebbi daga tabarbarewar tsaro, farfado da noma, da kare muradun al’umma, in ji rahoton Channels TV.

Ya musanta zargin cewa ya fito takara saboda wani burinsa kawai, yana mai cewa manufarsa ita ce sake gina jihar ta hanyar ingantaccen tsarin jagoranci.

Kara karanta wannan

'Mutane da yawa sun mutu,' Tinubu ya dauki muhimmin alkawari ga al'ummar Filato

Tsohon ministan ya bayyana cewa 67.6% na yaran jihar ba sa zuwa makaranta, wannan, a cewarsa, na daga cikin abubuwan da zai mayar da hankali a kansu.

Abubakar Malami ya bayyana cewa zai kawo ci gaba a jihar Kebbi idan ya lashe zaben gwamna.
Taswirar jihar Kebbi da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Matsalolin lafiya da tsaro a jihar Kebbi

Malami ya jaddada cewa rahotannin lafiya sun nuna cewa 81.5% na yara 'yan kasa da shekaru biyar na fama da zazzabin cizon sauro, yayin da 71% na mata masu juna biyu ba sa samun kulawar lafiya a yankunan karkara.

A wani rahoton Daily Post, tsohon ministan ya ce sama da 72% na mazauna jihar Kebbi suna rayuwa ne cikin tsananin talauci.

A bangaren tsaro, ya ce hare-haren ’yan bindiga daga 2021 zuwa 2025 sun yi sanadin rasa rayuka da dama, ciki har da sace mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi.

An sace daliban makarantar Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hari makarantar sakandaren kwana ta mata (GGCSS) Manga, da ke jihar Kebbi a daren Litinin.

'Yan bindigar sun kutsa cikin makarantar dauke da makamai, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar da ke kare dalibansa.

Kara karanta wannan

'Ka da a ziyarci kabarina': Tsohon gwamna ya ba da wasiyyar yadda za a birne shi

Wata mata da lamarin ya faru a yankin da take, ta bayyana cewa miyagun sun kwashe tsawon lokaci sun ta'asa, kafin awon gaba da dalibai mata masu yawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com