Takaitaccen tarihin ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami SAN
An haifi ministan shari'a na Najeriya kuma lauyan koli na kasa na yanzu, Abubakar Malami, a ranar 17 ga watan Afrilun shekarar 1967 a karamar hukumar Birnin Kebbi wadda ta kasance babban birnin jihar Kebbi.
Ya fara karatunsa na zamani a mataki na farko a makarantar Nassarawa Firamare da ke Birnin Kebbi kafin ya wuce College of Arts and Arabic Studies inda ya kammala karatunsa na Sakandire.
Malami ya kammala karatunsa na digiri a jami'ar Usman Danfodio a shekarar 1991 a fannin nazarin shari'a inda ya samu kwarewa ta zama lauya a shekarar 1992.
A shekarar 1994 ne Malami ya yi karatun digiri na biyu a jami'ar Maiduguri a fannin nazarin kula da kuma shugabancin al'umma wato Public Administration.
Kasancewarsa kwararren lauya, Malami ya yi aiki a matsayin lauyan kuma majistire a jihar Kebbi, hakazalika ya kasance mashawarcin a kan harkokin shari'a ga tsohuwar jam'iyyar CPC ta kasa, Congress for Progressive Change.
Ya samu karin girma inda ya zamto babban lauyan kasa wato SAN (Senior Advocate of Nigeria) a shekarar 2008.
Malami ya bayar da gudunmuwa mai yawan gaske wajen kafa jam'iyyar APC a shekarar 2013, inda ya kasance cikin sahun wadanda suka shiga kuma suka fita a gwagwarmayar da aka yi ta hade tsaffin jam'iyyun CPC da kuma ANPP, All Nigeria Peoples Party.
A shekarar 2014, Malami ya yi takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, inda ya sha kayi a hannun gwamna Abubakar Atiku Bagudu yayin zaben fidda gwanin takara.
KARANTA KUMA: Ngige, Malami da sauran ministoci 10 da zasu maimaita mukamansu a zango na biyu
Bayan samun nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zaben kasa na 2015, ya nada Malami a matsayin Ministan Shari'a kuma Lauyan kolu na kasa.
Nadin mukamin da Malami ya samu a ranar 11 ga watan Nuwamban 2015, ya sanya ya kasance mafi kankanta ta fuskar shekaru a cikin jerin 'yan majalisar zantarwa ta gwamnatin Buhari.
Bayan lashe zabensa a wa'adi na biyu da aka gudanar a bana, shugaban kasa Buhari a ranar Laraba 21 ga watan Agusta, ya rantsar da Malami a matsayin ministan shari'a kuma lauyan kolu na kasa karo biyu cikin jerin ministoci 43 da ya nada a sabuwar gwamnatinsa.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng