PDP Ta Sake Rikicewa: Tsohon Gwamnan Kogi Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Idris Wada, ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar APC, wanda hakan ke nufin ya fice daga PDP
- An bayyana cewa shigar Wada cikin APC ta nuna sabuwar babin siyasa da ke ƙara karfafa tasirin jam’iyyar a jihar Kogi
- Ana sa ran gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, na shirin karbar Wada da magoya bayansa a hukumance cikin APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Idris Ichalla Wada, tsohon gwamnan Kogi, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki a jihar da kasa baki daya, watau APC.
Wada ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar ne a ranar Asabar a gidansa da ke Odu, cikin Karamar Hukumar Dekina ta jihar Kogi.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Kogi ya koma APC
Hakan ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan ya bar jam’iyyar PDP a hukumance yayin da yake fara sabon shafi na siyasar sa, in ji rahoton TVC News.

Kara karanta wannan
PDP ta rikice: Gwamnoni 2 sun nesanta kansu daga korar Wike, Fayose daga jam'iyya
David Alfred-Dogwo, mai taimaka masa kan yaɗa labarai, ya bayyana cewa Capt. Idris Wada na da kwarin gwiwa game da makomar siyasar sa a APC.
Ya ce kodayake bikin ya kasance gajere ne, muhimmancinsa ya nuna cikakken shigar Wada cikin jam’iyyar tare da karfafa tasirin APC a yankin Kogi ta Kudu.
Ya bayyana cewa manyan shugabannin jam’iyyar APC, magoya baya da masu masa addu’a daga sassa daban-daban na Dekina sun halarci taron.
Sauya shekar Wada ta kara karfin APC
Mai taimaka wa Wada ya ce wannan sauyi zai taimaka wa jam’iyyar wajen kara karfi a Dekina da kuma kara shirye-shiryen APC wajen tunkarar zabubbukan nan gaba a jihar.
Ya kara da cewa hakan zai kuma karfafa goyon bayan jam’iyyar ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Wada ya rike kujerar gwamnan Kogi daga Janairu 2012 zuwa Janairu 2016 a karkashin PDP, amma ya gaza lashe zaben tazarce.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: PDP ta fatattaki Wike, tsohon gwamna da wasu da ke kawo mata cikas
INEC ta ayyana zaben Kogi da aka gudanar a ranar 21 ga Nuwamba 2015 a matsayin wanda bai kammalu ba, wanda hakan ya kai ga sake shirya sabon zabe a ranar 5 ga Disamba 2015.
Dan takarar APC na wancan lokaci, Abubakar Audu, ya rasu a ranar 22 ga Nuwamba — kwana guda bayan gudanar da zaben farko.
A karshe, bayan gudanar sabon zabe, hukumar INEC ta bayyana dan takarar maye gurbin APC, Yahaya Bello, a matsayin wanda ya ci zaben.

Source: Twitter
Gwamna Ododo zai tarbi Wada da magoya bayansa
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, na shirin karbar Wada da magoya bayansa a hukumance cikin jam’iyyar APC, in ji rahoton The Authority.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan labarai, Ismaila Isah, ya fitar, an ce za a yi taron tarbar sauya shekar ne a ranar Litinin a dandalin Muhammadu Buhari Square da ke Lokoja.
Taron zai samu halartar manyan shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da kasa, inda za a tabbatar da shigowar Wada cikin jam’iyyar.
Abia: Tsohon gwamna ya koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Abia, Sanata Theodore Orji ya mika takardar murabus ga shugaban jam'iyyar PDP a jiharsa.
Sanata Orji wanda ya mulki jihar Abia na tsawon shekaru takwas, ya ce ya yanke shawarar fita daga PDP ne bayan tattaunawa da abokan siyasarsa.
Wannan na zuwa ne a ranar da jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Ambasada Umar Damagum ta fara babban taro na kasa a Ibadan, jihar Oyo.
Asali: Legit.ng
