Wada ne ainihin ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP – Kotun daukaka kara

Wada ne ainihin ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP – Kotun daukaka kara

A yayin da ake fama da cutar COVID-19, babban kotun daukaka kara da ke garin Abuja ya zauna a game da shari’ar da ake yi tsakanin ‘ya ‘yan PDP a zaben gwamnan jihar Kogi.

Kotun daukaka karan ya tabbatar da ingancin tsayawa takarar Injiniya Musa Wada a zaben da aka yi a karshen shekarar 2019. Alkalai sun yanke hukunci ne a cikin farkon makon.

Alkali Ibrahim Muhammad Saulawa da Joseph E. Ekanem da Yasir Nimpar su ka saurari karar da aka shigar inda ake korafin cewa jam’iyyar PDP ba ta shirya zaben fitar da gwani ba.

Alkali mai shari’a Saulawa da sauran abokan aikinsa sun ruguza hukuncin da aka yi a baya, su ka tabbatar da cewa PDP ta gudanar da zaben cikin gida sarai wajen fito da Idris Wada.

“An rusa duk wani hukuncin da aka yanke da ya ce ba a yi zaben tsaida ‘dan takara a jam’iyyar PDP, kuma wanda ake tuhuma ba shi ba ne ‘dan takarar jam’iyyar ba.” Inji kotu.

KU KARANTA: Dino Melaye ya bada gari kafin a kammala zaben Kogi ta Yamma

Wada ne ainihin ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP – Kotun daukaka kara

Kotu ta ce an bi doka wajen ba Wada tikitin takara a Kogi
Source: Facebook

Alkalan sun bada hukuncin cewa babu shakka jam’iyyar PDP ta bi matakan da doka ta ce wajen fito da wanda zai rike mata tuta, don haka takarar Injiniya Wada ba ta tashi a banza ba.

Abubakar Mohammed Ibrahim Idris shi ne ya shigar da wannan kara mai lamba ta CA/A/193/2020 a kotun da ke zama a Abuja. A jiya Talata aka zauna a kan shari’ar.

Alhaji Abubakar Idris ya fara gabatar da kara ne a babban kotun tarayya da ke jihar Kogi a watan Satumban 2019, ya na kalubalantar yadda PDP ta ba abokin adawarsa tutar takara.

Wannan ya na cikin nasarar da Wada ya fara samu a gaban kotu duk da cewa ya sha kashi a zaben Nuwamban baran. Gwamna mai-ci Yahaya Ballo na jam’iyyar APC ne ya yi nasara.

Tuni dai Injiniya Wada ya shigar da kara a kotun sauraron korafin zabe ya na kalubalantar nasarar da hukumar INEC ta ba jam’iyyar APC da kuma ‘dan takararta gwamna Bello.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel